An sake yin garkuwa da mahaifiyar Samson Siasia da kannen sa biyu

0

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ’yan bindiga sun sake arcewa da mahaifiyar fitaccen tsohon dan kwallon nan wanda ya buga wa Najeriya, Samson Siasia.

Dama kuma shekaru hudu da suka gabata an taba yin garkuwa da ita, sai da aka biya makudan kudade kafin su sake ta.

An yi garkuwa da Ogere Siasia wajen karfe biyu na dare a garin Odoni da ke cikin Karamar Hukumar Sagbama ta Jihar Bayelsa.

An kuma tabbatar da cewa masu garkuwar sun yi awon-gaba da wasu kannen Siasia biyu, suka hada da mahaifiyar sa, su ka yi gaba.

Wani kanin Siasia mai suna Dennis, ya tabbatar da cewa an yi garkuwa da mahaifiyar ta su da kuma ‘yan uwan sa biyu.

Yayin da har lokacin da ake rubuta wannan labari, ba a ji komai daga bakin wadanda suka yi garkuwar da ita ba, Kakakin Yada Labarai na Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bayelsa ya ki cewa komai domin jin ta bakin sa.

An kama Ogere a daidai lokacin da hare-hare da garkuwa da jama’a ya ke kara muni a fadin kasar nan.

A kullum ‘yan bindiga na ci gaba da datse kan manyan titina, sun a tare matafiya, ana garkuwa da su.

A kauyuka kuma ana ci gaba da hare-haren kisan su, yin garkuwa da su da kuma kona musu matsugunai.

Dennis ya ce an sanarwa Siasia halin da mahaifiyar sa ke ciki, kuma tuni ya na tuntubar jami’an tsaro domin ceto mahaifiyar sa.

Siasia na cikin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya da ciwo kofin Afrika a kasar Tunisia, cikin 1994.

Kuma ya na cikin kungiyar ne Najeriya ta samu zuwa gasar cin kofin duniya a karo na farko, a kasar Amurka, cikin 1994.

Siasia ya taba zama kocin kungiyar Super Eagles na wani lokaci.

Share.

game da Author