Rikici ya kaure a majalisar Tarayya a dalilin zaben sabon shugaban masu rinjaye.
Rikicin ya kaure ne bayan kakakin majalisar Femi Gbajabiamilla ya b’yan ayyana suna Ndudi Elumelu a matsayin shuagaban marasa rinjaye na majalisar.
Abin bai yi wa ‘yan Jam’iyyar PDP dadi cewa ba sunan Elumelu aka mika wa kakakin a matsayin sabon shugaban marasa rinjayen.
Jam’iyyar PDP ta aika da sunan Kingsley Chinda a matsayin shugaban marasa rinjaye a majalisar, amma Kakakin majalisar ya ki ambata sunan sa ya zabi Elumelu.
An rita hauragiya tsakanin mabobin sannan wani ma har ya nemi ya dauke sandan iko.
Discussion about this post