A yau Litinin ne jami’an ’yan sanda suka gurfanar da Sanata Elisha Abbo a kotu, bayan zargin sa da aka yi da dad-dalla wa wata matar aure mari a cikin kantin saida azzakarin roba a Abuja.
Za a gurfanar da shi ne a Kotun Majistare da ke Zuba, kamar yadda rundunar ’yan sandan Abuja ta bayyana.
Abbo ya na wakiltar Shiyyar Adamawa ta Arewa ce. Premium Times ce ta fallasa wani bidiyon da aka nuno shi ya zubar da kimar sa ta sanata ya rika zabga wa matar aure mari a kantin sayar da kayan mata.
An tabbatar da cewa Abbo ya je kantin sayar da azzakarin robar ne tare da wasu mata uku, wadanda aka tabbatar da cewa babu matar sa a cikin su.
Kakakin Yada Labarai na Rundubar ’Yan Sandan Abuja, Anjuguri Manzah, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sanda sun shigar da tuhuma a kan Sanata Abbo, bayan da suka kalli bidiyon da aka nuno shi ya na zabga wa matar mari har a cikin idanun ta.
An watsa bidiyon a ranar 2 Ga Yuli, 2019, kuma nan da nan ya game duniya, har aka rika yi wa sanatan tofin Allah-tsine.
Duk da cewa Abbo ya fito ya bayar da hakurin abin da ya faru, hakan bai hana ‘yan sandan Abuja gayyatar sa ba. Amma dai daga baya an bayar da belin sa bayan daukar wani dogon lokaci a hedikwatar su ta Abuja.
Ba a dai sani ba ko zai amince a gaban alkali cewa ya aikata laifin da ake zargin sa. Amma dai Anjuguri ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa bayanin da yayi lokacin da ya ke bayar da hakuri, ya isa ya zama hujja a gaban kotu cewa sanatan ya ci zarafin matar.
An tabbatar da cewa za a gurfanar da shi kafin karfe 12 na ranar yau Litinin a kotu.
Jami’an kotun sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa akwai batun gurfanar da Sanata Abbo a cikin jerin shari’un da kotun ta Zuba za ta saurara a yau. Amma dai har kusan 12 na ranar yau din ba a kai ga gurfanar da shi a kotun ba tukunna.