An dakatar da dukkan albashi da alawus-alawus na Hadiman Shugaba Muhammadu Buhari da na Mataimakinsa, Yemi Osinbajo. PREMIUM TIMES ta tabbatar da haka jiya Laraba.
Wadanda aka dakatar da dukkan albashi da alawus din na su, sun hada da dukkan wadanda wa’adin aikin su ya kare daga ranar 28 Ga Mayu, 2019, kuma ba a sabunta musu takardar ci gaba da aiki tare da Shugaba Buhari ko Mataimakin sa Osinbajo ba.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa wadannan hadimai na cikin jidali, domin babu wanda aka biya albashin watan Yuni, kuma an dakatar da dukkan alawus-alaus na su.
Sama da wata daya kenan tun bayan sake rantsar da Buhari karo na biyu, amma har yau bai sabunta nadin na su ba kuma bai kore su ya nada sabbi ba.
Buhari bai sallami ko daya daga cikin su ba, amma kuma ya bar su a kewaye da shi su na ci gaba da yi masa hidima shi da Osinbajo.
Wannan katankatana ta rashin sallamar hadiman shugaban kasa da kuma kin nada wasu, ta haifar da surutai a kasar nan, har lauyoyi na cewa haramun ne a tsarin dokar kasar nan a bar wadannan hadimai na ci gaba da aiki bayan wa’adin su ya cika a kan aiki.
Sama da hadimai 100 tare da iyalan su ne suka samu kan su cikin wannan kiki-kaka, ciki har da manyan hadiman Buhari na yada labaai, Garba Shehu da Femi Adesina.
Wata majiya a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa hadimai uku ne kadai wannan rakamniya ba ta shafa ba.
Wadanda abin bai shafa ba sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapaha, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari da kuma Mataimakin sa, Adeola Ipaye wanda ke Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa.
Aiki Babu Albashi
Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya tabbatar da cewa ma’aikatan da ke bangaren kudade a ma’aikatun gwamnatin tarayya sun cire sunayen hadiman Buhari da na Osinbajo kusan 100 daga cikin tsarin biyan albashi.
Wasu hadimai sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa sun karbi albashin watann Mayu, wanda suke kallo shi ne albashin su na karshe.
Sannan kuma wasu ma’aikatan gwamanatin tarayya sun tabbatar da cewa ba su biya hadiman albashin watan Yuni ba.
Baya ga albashi, wannan jarida ta gano hatta sauran alawus kamar kudin tafiye-tafiye da na tsaraba duk an dakatar daga biyan hadiman.
Wannan sabalula ta fara bayyana ne tun cikin makon jiya a lokacin da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ke kokarin tafiya ziyara Amurka.
Osinbajo ya cika da mamaki yayin da aka sanar da shi cewa tafiya tare da hadiman sa ba za ta yiwu, domin an dakatar da albashi da dukkan alawus-alawus din su, har da kudaden tafiye-tafiye duka.
Wannan ya sa tilas sai dai Osinbajo ya shiga ya fita, ya kukuta, ya samo kudaden da ya yi amfani da su wajen daukar nauyin tafiya tare da wasu kalilan daga cikin hadiman na sa.
Irin haka ma na shirin faruwa ga Shugaba Buhari a lokacin da zai tafi kasar Jamhuriyar Nijar, domin PREMIUM TIMES ta gano cewa zai tafi ne da wasu hadimai ‘yan kalilan, ba kamar yadda ya saba tafiya da garken su ba.
Ana kokarin Gyarota
Kakakin Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willy Bassey, ya ki cewa komai a kan ba tun.
sai dai kuma ya yi karin hasken cewa hakkin ofishin Hukumar Raba Kudade da Tsara Alabashi ce ta tuntube su a kan batun.
Sai dai kuma wani babban jami’in da bai amince a bayyana sunan sa ba, ya shaida cewa ana nan ana kokarin warware matsalar, domin ana kokarin sabunta wa wasu hadiman karin wa’adin aiki a wannan sabiwar gwamnati.