A cigaba da gasar cin Kofin Nahiyar Afrika da ake bugawa a kasar masar, Aljeriya ta lallasa Najeriya da ci biyu da daya.
Wannan wasa tayi zafin gaske, inda tun a farkon rabin lokaci Najeriya ta ci kanta da kanta ta hannun mai tsaron gidan ta Efiong.
A haka dai aka yi ta doka tamola anata gwabzawa kamar ba za a yi ba sai kwatsam Najeriya ta samu bugun daga kai sai gola.
Dan wasa Ighalo ya ya zura kwallon a ragar Aljeriya a daidai minti 75 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Bayan an kara minti 4 bayan cikan lokacin wasa, sai Aljeriya ta samu firiki.
Fitaccen dan wasan su Riyad Mahrez, ya yi kwance-kwance ya doka kwallon diii sai cikin ragar Najeriya.
An dai tashi wasa 2 da 1.
Aljeriya za su kara da Senegal a wasan karshe, inda ita kuma Najeriya zata kara da Tunisia a wasan wanda zai zama na uku.