Akwai yiwuwar El-Zazzaky da Matarsa Zeenat za su iya mutuwa a tsare – Dan El-Zazzaky

0

Daya daga cikin ‘ya’yan jagoran kungiyar Shi’a a Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky, Mohammed Zakzaky ya bayyana cewa akwai yiwuwar mahaifinsa da mahaifiyarsa su rasu a tsare a dalilin irin halin da ya gansu a wajen da gwamnati take da tsare su.

Mohammed yace iyayen sa na matukar bukatan a duba lafiyar su domin duk suna cikin damuwa da rashin lafiya mai tsanani.

” Mahaifina na cikin matsanancin hali na rashin lafiya kuma jami’an SSS sun hana likitocin kwarai su duba shi. Yana kwance bashi da lafiya. Ita ma mahaifiyata ta na a kwance cikin halin rashin lafiya.

” Likitoci sun ce lallai sai an kai shi asibitin kwarai da za akula dashi sosai ne zai samu lafiya amma gwamnatin Najeriya taki yarda a yi haka.

Idan ba a manta ba tun a shekarar 2015 ne ake tsare da El-Zakzaky sannan har yanzu ba a sake shi duk da awani lokaci a baya Kotu ta ce a sake shi amma hakan bai yiwuba.

Sannan kuma har yanzu magoya bayansa na gudanar da zanga-zanga a musamman babban birnin tarayya, Abuja domin nuna fushinsu ga tsare El-Zakzaky da gwamnati take yi da sannan kuma kira ga a sake shi yaje ya nemi magani.

Share.

game da Author