Akalla mutane 14 aka tabbatar sun rasu a ruftawar bene a Jos

0

Nurudeen Musa, jami’in Hukumar NEMA ta Kasa ya bayyana cewa akalla mutane 14 ne aka tabbatar sun rasu a rugujewar wani gidan sama a garin Jos.

Musa ya ce baya ga mutanen da aka tabbatar sun rasu, an ciro wasu 3 da suka samu mummunar rauni a jikkunan su amma tuni an garzaya dasu asibiti.

A ranar Litinin ne wani gidan sama mai hawa uku ya rufta da mutane make dam a ciki. Shi dai wannan gidan sama, akai shaguna da dama da ake hada-hada da kasuwanci a ciki.

Wannan abin tausayi da tsahin hankali ya auku ne ranar Litini da karfe biyar na yamma a layin mahauta dake karamar hukumar Jos ta Arewa jihar Filato.

Bayanai sun nuna cewa mutane da dama sun rasu a wannan hadari.

Idan ba a manta a kwanakin baya wani bene shima irin haka wanda makaranta ne a Legas ya rufta da daliban makaranta.

Al’amarin ya faru ne a kan titin Massey Street, dake Karamar Hukumar Lagos Island, da ke Legas.

Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai mutane da dama cikin sa, har da daliban da ke karatu a lokacin da abin ya faru.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an zakulo dalibai 10 da gini ya danne.

Share.

game da Author