AIKIN DAN SANDA: Ba za a dauki masu zane a jiki da makakku ba

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Enugu ta tabbatar da cewa ba za ta dauki duk matashin da ke da zane a jikin sa kamar bayan kwarya ba.

Haka kuma ta bayyana cewa duk wanda ke da alamar kan sa da motsi, ko kwarkodiyo, ko shagirigirbau ko mai alamun buguwar kwayoyi, duk ba za su samu shiga aikin dan sanda ba.

Kakakin Yada Labarai na Rundunar Enugu, Ebere Amaraizu ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai ranar Talata a Enugu.

Y ace ana yi wa matasan da aka daukin sunayen su horon atisayen gane gejin kuzarin kowa ne kafin a dauke shi ko kuma kafin a yi watsi da shi.

Ya ce za a dauki mako daya cur ana gudanar da atisayen, kamar yadda Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda ta Kasa (PSC) ta goyi bayan gudanarwa.

An fara 1 Ga Yuli, kuma za a kammala ranar 6 Ga Yuli.

Ya ce ana gudanar da tantancewar a tsanaki, domin dukkan wadanda suka cika fam din neman aikin dan sanda daga dukkan kananan hukumomin jihar 17, akwai ranakun da aka kebe domin a yi musu.

Ya ce kowace karamar hukuma ta san ranar da za yi mata, don haka babu bukatar yin cinkosu har abubuwa su dagule.

Hukumar PSC ta fitar da sunayen matasa 2,945 masu neman a dauke su aikin dan sanda. Daga cikin su ne za a tankade, a rairaye, a dauki na dauka, a zubar da na zubarwa.

Share.

game da Author