ABUJA: Hanyoyi 15 Da Minista zai bi ya dawo da birnin tarayya cikin hayyacin Sa

0

Kusan mafi yawan masu sharhi dangane da Babban Birnin Tarayya, Abuja, su na ikirarin cewa an dade ba a yi talasurun Minista kamar Bello Mohammed, wanda ya sauka cikin Mayu ba.

Saboda rokon-sakainar-kashin da ya yi wa Abuja, mutane da dama sun yi ta murnar saukar da ya yi a karshen wa’azin sa, an ana ta addu’a kada Allah ya sa Shugaba Muahmmadu Buhari ya sake nada shi.

Sai dai kuma murna ta koma ciki, ganin sunan Mohammed Bello a jerin sunayen sabbin ministoci, kuma tuni har Majalisar Dattawa ta tantance shi, ba tare da yi masa tambaya ko daya ba.

Ganin yadda Abuja ta lalace da yawan aikata laifukan sata, fashi, garkuwa, kwace da kuma fizge gami da rashin tsafta a birnin tarayya, PREMIUM TIMES ta zayyano wasu hanyoyi 15 da ta ke ganin cewa idan aka dawo Bello Abuja, to yin amfani da shawarwarin zai sake dawowa Abuja da martabar ta.

1. Gyara wutar lantarki ta sola wadda ke haskaka fitilun kan titi. Rashin haske a yawancin manyan titinan Abuja ya haifar da masu aikata laifuka da dama.

2. Gyara fitilun danjoji masu bada hannu, wadanda rashin aikin su da lalacewar da suka yi na haddasa hadurra sosai a Abuja.

3. Dakile matsalar tsaro tare da gano fitattun wuraren da masu aikata laifuka ke watayawar su yadda suka ga dama a Abuja.

4. Inganta hasken wutar lantarki a Abuja, ta yadda zai zama kamar sauran manyan biraren kasashen Afrika.

5. A kawar wuraren tula shara da ce ciki da gefen Abuja. A kuma hana jibge kwandon shara kan titi ko cikin unguwa barkata, ba tare da kwashewa ba.

6. A maida tsarin zirga-zirgar motocin haya zuwa na zamani ta yadda za a kawar da fashi da sata da fasinjoji masu hawan motocin haya ke fuskanta.

7. A gyara kyamarar CCTV da aka taba kafawa a ko’ina cikin fadin Abuja. Idan ba za su gyaru ba kuwa, to a gaggauta kafa wasu.

8. A gig-gina dakunan wanka da bayan-gida har ma da na tafi-da-gidan la, yadda za a magance kazantar masu tula kashi a cikin duhun bishiyoyi a gefen titi cikin Abuja.

9. Minista ya kai daukin inganta kayan more rayuwa a kauyukan Abuja inda ake zama irin na sansanin-gudun-hijira, wato ‘slumps’.

10. Kula da gyaran manya da kananan hanyoyin ruwa da kuma hanyoyi da mahadar bututun bayan gida.

11. Inganta tsarin samar da ruwan sha ta hanyar shigo da kamfanoni masu zaman kan su yin hadin-guiwa da Hukumar FCT.

12. A yi gaggawar kammala titinan da ake jan-kafa wajen kammala aikin su.

13. A hana makiyaya shigowa kiwon shanu a cikin Abuja.

14. A hana barace-barace a cikin kasuwa, kan titi da kuma bakin danja.

15. A hana masu tallace-tallace barkatai a cikin Abuja.

Share.

game da Author