Abin da ya hana a fara aiki da sabon tsarin albashi gadan-gadan – Shugabar Ma’aikata

0

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Winifred Oyo-Ita, ta bayyana cewa babbar matsalar da ta hana a fara amfani da sabon tsarin karin albashi, ita ce yawan bukatun da Kungiyar Kwadago ta Kasa ke gabatar wa Gwamnatin Tarayya.

Oyo-Ita ta yi wannan bayani ne a jiya Litinin a Abuja a wurin taron kwanaki biyu na manyan ma’aikatan tarayya da ke ofishin ta.

Sai dai kuma ta kara da cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago daban-daban.

An shirya taron ne domin nazari da bayar da horo a kan tsare-tsaren Sabon Tsari da Fasalin Aiki na shekarun 2017 zuwa 2020 na Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, wato (FCSSIP).

Ta ce wadanan bukatu da Kungiyoyin Manyan Ma’aikatan Gwamnati su ka gabatar, na daga cikin batutuwan da ake sa-toka-sa-katsi a kan su.

Ta ce saboda ba a so a ci gaba da bata lokaci ce gwamnati ta amince da fara biyan kananan ma’aikata tun a cikin watan Afrilu.

Daga nan sai ta ce gwamnatin tarayya ba za ta bari bukatun manyan ma’aikata su shafi fara biyan masu kananan karfi a cikin ma’aikata ba.

Tun a farkon 2018 ne aka sa ran za a fara biyan tsarin mafi kankantar albashi na naira 30,000 kamar yadda gwamnati ta sha alwashi a baya.

Sai dai kuma karshen 2018 din sai gwamnati ta ce sai cikin 2019.

Share.

game da Author