Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara wa jihohin kasar nan kason kudaden da aka ba su a duk karshen wata, domin su fi jin dadin biyan akarin albashi cikin sauki.
Har yanzu dai ana sa-toka-sa-katsi dangane da batun biyan karin albashi zuwa naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi.
Masari ya ce jihar sa ba ta da matsalar kasa biyan karin albashin ma’aikata, domin kowa ya san abin da ta ke samu a kowane wata.
Ya yi wannan magana ce jiya Juma’a, a lokacin da ya karbi shugabannin kungiyar kwadago ta Jihar Katsina.
Ya ce gwamnatin jihar za ta buda yadda tsarin biyan albashin ya ke, sannan kuma ta yi aikin nazarin sa tare da bangaren tsara albashi da kasafin kudaden ayyuka na jihar domin a fara aiki da shi sabon tsarin.
“Idan aka kammala fito da tsarin karin albashin, za a gayyaci Kungiyar Kwadago ta jihar Katsina ita ma ta tabbatar da shi.
“Saboda ni dai a gaskiya ba ni da wata matsala da biyan sabon tsarin albashi. Domin duk kun san abin da ake bai wa jihar nan kowane wata daga gwamnatin tarayya.”
Daga nan ya bayyana musu cewa ya na kan kokarin ganin an gyara M a’aikatar Samar da ruwan sa domin magance matsalar rashin ruwa da Katsina ke fuskanta.
Ya ce an rigaya an gyara madatsar ruwa ta Ajiwa, kuma an saka kayar tsaftace ruwa domin gaggauta samar da ruwa.
Discussion about this post