Tsohon Gwamnan Jiyar Osun, Rauf Aregbesola,, ya yi alkawarin cewa idan ya zama minista zai rura wutar kara narka wa attajirai haraji, domin gwamnati ta kara samun kudin shiga.
Ya yi wannan furucin ne a gaban Majalisar Dattawa, lokacin da ake tantance shi a matsayin sabbin ministocin da Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sunayen su domin neman amincewa.
Furucin na daga cikin amsoshin da ya bayar a lokacin da wasu dattawan Majalisar ke masa tambayoyi dangane da hanyoyin samun kudin shiga.
Ya ce tunda ana fuskantar rashin wadattaun kudaden shiga, saboda manyan bukatu sun yi wa Najeriya yawa, to idan ana so harkokin inganta tattalin arziki su kara inganta, sai an kara lafta wa attajirai haraji.
Ya ce zai shiga a sahun gaba wajen kokarin an shigo da abin da ya kira ‘harajin masu hannu da shuni’, ga wadanda suka mallaki tarin dukiya.
“Zan bayar da fatawar narka wa manyan attajirai harajin jiki-magayi.” Sannan ya kara da cewa su wadannan attajirai da suka mallaki bilyoyi, za su biya haraji fiye da adadin da suke biya a yanzu, matsawar shugaban kasa ya amince da haka.
Aregbesola ya ce akwai rata mai tsananin gaske tsakanin attajirai da fakirai a Najeriya.
Idan ba a manta ba, rahoton Cibiyar Oxfam ya bayyana cewa mashahuran attajiran Najeriya su 5 sun mallaki dalar Amurka biliyan 29.9, wato su na da adadin da ya zarce kasafin kudin Najeriya na shekarar 2017.
“Sai wanda ya fi kowa kudi a Najeriya (Aliko Dangote) ya shafe shekara 47 ya na kashe dala milyan 1 a kowace rana sannan kudin da ya mallaka za su kare.
Kasar Brazil ce aka kwatanta da Najeriya, wadda ita kuma kididdiga ta tabbatar da cewa wasu mutane kashi 5 bisa 100 na kasar sun mallaki dukiya wadda ta fi ta sauran kashi 95 bisa na al’ummar kasar sama mutane milyan 100.