Darektan Yada Labarai na Ƙungiyar IMN da ka fi sani da Shiite ya ce Haramta Ƙungiyar Shiite a Najeriya ba zai taɓa tasiri ba a garesu domin ba zai hana su ci gaba da abinda suke yi a matsayin su na Ƙungiya ba.
Musa yace koda yake bawai yana magana ne da yawun Ƙungiyar ba, yana magana ne a matsayin sa na jigo ƙuma ɗan Ƙungiya.
” Wannan hukunci na kotu ba zai yi wani tasiri ba a garemu. Ina so in tabbatar muku cewa bazai hana yin abinda muka sa a gaba ba. Ina hukuncin kotu akan ɗaruruwan mutanen mu da sojoji da jami’an tsaro suka kashe.”
” Babu doka a ƙasarnan da ya hana mutane yin addininsu. Saboda haka idan har ance za a haramtamu toh ashe za a hana mu yin sallah kenan, ko kuma zuwa aikin Hajji.
” Ay ba sai sun nema kotu ta yardan musu su haramta mu ba. Gwamnatin Najeriya bata bin umarnin kotu. Da suka tafi Zariya suka kashe mana dubban mutane, ay basu nemi izinin kotu ba, haka kuma waɗanda aka kashe a Abuja ma ay ba a nemi izinin kotu ba.
Lauyoyi sun rabu bisa haramta Ƙungiyar Shiite
Wani lauya, Johnmary Jideobi, ya bayyana cewa kokarin haramta ƙungiyar shiite a Najeriya karya doka ce domin a kundin tsarin mulkin Najeriya ya rubuce ƙarara cewa kowa na da ikon yin addinin sa ba tare da tsangwa ba.
Jideobi yace dole ne fa idan har sai an haramta ƙungiya dole sai an kai wannan ƙungiya kotu sannan kotu ta tabbatar da ƙungiyar ta’adda ce kafin a iya haramta shi.
” Amma kotu bata ikon haramta ƙungiya irin haka.”
Shi ko Lauya Monday Ejeh bayyana cewa yayi babu dalilin da zai sa ace wai gwamnati ba za ta haramta ƙungiyar da ke karya doka kamar ƙungiyar Shiite.
Dokar ƙasa ya ba gwamnati damar haramta ƙungiyar da ke irin ayyuƙan da Shiite ke yi a ƙasarnan. Damarda doka ta bada na ƴanci ga ɗan ƙasa na walwala da yin addininsa yadda ya yake so bai kuma zama dole ba ace a dalilin haka wani yana muzguna wa wani da sunan dama da doka ta bashi ba
” Bisa ga dabiun su da abubuwan da suke yi na karya doka suma duk gwamnatin da ta haramtasu tayi daidai bisa dokar ƙasa.
Idan ba a manta ba babban kotun shari’a da ke Abuja ta ba gwamnatin Najeriya dama ta haramta kungiyar Shiite a kasarnan.
Mai shari’a Nkeonye Maha na babban Kotun Abuja ta bayyana a takarda cewa daga yanzu kada wani ya bayyana kansa a matsayin dan Shi’a a kasarnan.
Sannan kuma ta bayyana cewa Antoni Janar din Kasa zai saka wannan takarda a jaridun kasar nan har guda biyu kafin a kaddamar sannan gwamnati ta tabbatar da haka a dokar kasa wanda shugaban kasa zai rattaba hannu a kai.
PREMIUM TIMES ta ruwaito labarin shirin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na bayyana ƙungiyar IMN, wato Shi’a a matsayin haramtaccen ƙungiya a ƙasarnan.
Hakan ya biyo bayan bayanan kud-da-kud ne da PREMIUM TIMES ta jiyo daga majiya masu ƙarfi.
Rahoton ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa Buhari zai tabbatar da haka kuwa shine ganin irin yadda ƴan shi’a suka canja salon zanga-zangar, ya koma hare-hare da arangama da suke yi da ƴan sanda da har sai anyi jina-jina a duk lokacin da suka fito.
Discussion about this post