Shugaban hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa (NAFDAC) Moji Adeyeye ta gargaddi mutane da su nisanta kan su daga cin ganda ko kuma ponmo.
Adeyeye ta gargaɗi mutane ranar Juma’a a wata takarda da aka rabawa manema labarai a Abuja.
Ta yi bayanin cewa yin wannan gargaɗi ya zama dole ganin cewa wasu fasakwaurin ƴan kasuwa na siyar wa mutane fatar dabbobin da aka keƙe domin maida su takalma,jaka da sauran su.
Adeyeye ta ce fatar dabbobin da aka keɓe irin haka na cutar da kiwon lafiyar mutum saboda an zuba musu sinadarorin dake hana su lalacewa.
Ta ce akan kamu da cututtukan da suka haɗa da daji, ciwon ƙoda,ciwon hanta,cututtukan dake kama zuciya da sauran su idan har dai mutum ya ci irin waɗannan fatu.
Adeyeye ta kuma ce bisa ga rahoton bincike an shigo da fatun ne daga kasashen Lebanon da Turkey.
“A dalilin haka muke kira ga mutane da su guji cin ganda kokuma ponmo domin kare kiwon lafiyar su”
Duk da cewa NAFDAC na yin namiji kokari wajen ganin ta hana shigowa da sarrafa jabun magunguna da kayan abinci a kasar nan, NAFDAC ta ci gaba da kira ga mutane da su kiyaye da irin abinci da magungunan da suke siya domin wasu basu da kyau.