Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN), ta kori wasu jami’anta dake kula da tsaro a tashar jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas.
Hakan ya biyo bayan darewa fika-fikan jirgin AZMAN da wani ya yi ne a ranar juma’a.
Waɗanda aka dakatar sun haɗa da shugaban tsaro na hukumar, Mamman Mohamned, sauran sun haɗa da Oni Adedamola Abiodun, Owotor Kenneth Okezie da Badejo Adebowale Ayodele.
Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne a Filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed da ke Lagos, wani mutum da ba a san ko wane ba, ya yi kumumuwar shahadar-kuda, sai ga shi a kan fuka-fikin jirgin kamfanin AZMAN AIR.
Wakilin mu ya tabbatar da cewa al’amarin ya faru ne a lokacin da jirgin ya fara gungurawa ya na tafiya a kasa, kafin ya kai ga surmuyawa a guje har ya cira sama.
Wani fasinja ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa mutumin dai daga cikin jeji ya bullo, sai kawai aka ga ya nufo jirgin gadan-gadan a guje.
A lokacin da matukin jirgin ya hango shi, sai ya yi sauri ya tsaida jirgin, kuma ya kashe injin din jirgin.
Wani bidiyo da aka rika watsawa a soshiyal midiya ya nuna yadda mutumin ya na isa sai ya haye saman jirgin, sai ga shi har a kan fuka-fikin jirgi.
Wannan al’amari ya jefa dukkan fasinjojin cikin jirgin a cikin rudani da kidimewa.
Tuni dai jami’an kula da filin jirgin suka shawo kan lamarin.
Kakakin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Kasa, Henrietta Yakubu, ta tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa za su sanar da komai nan ba da dadewa ba.
An dai kama mutumin wanda ya haye fuka-fikin jirgin da ya yi niyyar tashi daga Lagos zuwa Fatakwal.
Sai dai kuma wannan lamari ya bar baya da kura, domin tuni aka dakatar da wasu manyan jami’an tsaron da ke lula da filin jirgin, har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Discussion about this post