Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta sanar cewa ashe wani ɗan asalin ƙasar Nijar ne ya ƙetaro yayi kwance-kwance ya mamayi jami’an tsaro ya dare can ƙololin fika-fikin jirgin AZMAN a Legas.
Kakakin rundunar, Joseph Alabi ne ya karanto haka a taron manema labarai.
Ya ce wanda aka kama ɗan asalin ƙasar Nijar ne mai suna Usman Adamu.
A ranar Asabar dinnan ne Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN), ta kori wasu jami’anta dake kula da tsaro a tashar jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas.
Hakan ya biyo bayan darewa fika-fikan jirgin AZMAN da shi Usman Adamu ranar juma’a.
Waɗanda aka dakatar sun haɗa da shugaban tsaro na hukumar, Mamman Mohamned, sauran sun haɗa da Oni Adedamola Abiodun, Owotor Kenneth Okezie da Badejo Adebowale Ayodele.
Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne a Filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed da ke Legas, Usman Adamu ya yi kumumuwar shahadar-kuda, sai ga shi a kan fuka-fikin jirgin kamfanin AZMAN AIR.
Wakilin mu ya tabbatar da cewa al’amarin ya faru ne a lokacin da jirgin ya fara gungurawa ya na tafiya a kasa, kafin ya kai ga surmuyawa a guje har ya cira sama.
Wani fasinja ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa Usman dai daga cikin jeji ya bullo, sai kawai aka ga ya nufo jirgin gadan-gadan a guje.
A lokacin da matukin jirgin ya hango shi, sai ya yi sauri ya tsaida jirgin, kuma ya kashe injin din jirgin.
Wani bidiyo da aka rika watsawa a soshiyal midiya ya nuna yadda mutumin ya na isa sai ya haye saman jirgin, sai ga shi har a kan fuka-fikin jirgi.
Wannan al’amari ya jefa dukkan fasinjojin cikin jirgin a cikin rudani da kidimewa.