Ƙungiyar kula da al’amuran likitoci ya yi wa sabbin likitoci 412 rajista

0

Ƙungiyar kula da al’amuran likitocin Najeriya (MDCN) ya yi wa sabbin dalibai likitoci 412 da suka kammala karatun a jami’o’in dake kasashen waje rajista.

An gudanar da wannan taron ne a makon da ya gabata a ɗakin taro ns ‘NAF conference center’ dake Abuja.

Jami’in kungiyar Abba Hassan yace daga cikin wadannan likitocin akwai likitoci cikakku 407, biyar kuma likitocin hakora.

“Likitoci 893 ne suka rubuta wannan jarabawan inda daga ciki 412 ne suka yi nasara.

Hassan ya kuma yi kira ga iyayen yara da su rika tantance ƙwarewar makarantun da suke tura ƴaƴan su a ƙasashen waje.

“Yin haka zai tabbatar da ingancin karatun su musamman bayan an dauke su aiki a kasar nan.

Hassan ya yi kira ga gwamnati kan ware kudade domin horar da masu koyan aikin likitanci sannan ya kuma yi kira ga gwamnatin jihohi kan inganta asbitocin dake jihar domin horas da masu koyan aiki a asibitocin.

Bayan haka babban bakon taron kuma sakataren ma’aikatan kiwon lafiya Shehu Sule ya yi kira ga MDCN dasu gyara matakan aikin likitanci a ƙasar nan.

Ya ce hakan zai taimaka wajen sajewa da sabbin dabarun aiyukka na zamani.

Rajistaran Ƙungiyar MDCN Tajudeen Sanusi ya yi wa sabbin ɗaliban gargadi kan ɓin sharuɗɗa da dokokin wannan aikin.

Share.

game da Author