Sakamakon wani buncike da aka yi game da sanin waɗanda suka fi kamuwa da cutar Ƙanjamau da Tarin Fuka ya nuna cewa fursinoni sun fi sauran mutanen da ba a tsare ba saurin kamuwa da da waɗanan cututtuka da kuma yawa idan akayi gwajin lissafi bisa 100 na yawan masƴ ɗauke da cutar.
Sakamakon wannan bincike ya nuna cewa adadin yawan fursinoni dake dauke da Ƙanjamau ya kai kashi 2.8 bisa 100 a inda kashi 1.4 bisa 100 na mutanen da basu a tsare a kurkuku ne ke ɗauke da cutar.
Ƙungiyar sa ido kan miyagun ƙwayoyi da manyan laifuka na majalisar dinkin duniya (UNIDC), Hukumar hana yaduwar cutar kanjamau ta kasa (NACA),Hukumar fursunoni ta kasa,Ma’aikatar kiwon lafiya, kungiyar ‘Heartland Alliance International,UNAIDS da USAID ne suka gudanar da wannan bincike.
An gudanar da binciken a kan fursinoni 2,511 dake tsare gidajen yari 12 a mazabu shida na kasar nan.
Sakamakon binciken ya ƙara nuna cewa a gidajen yarin dake Arewa ta Tsakiya ne aka fi samun madu ɗauƙe da wannan cututtuka da suke da aƙaƙla kashi 7.1.
Daga cikin fursinonin da aka gudanar da wannan bincike mata sun fi maza kamuwa da cutar domin kashi 6.9 bisa 100 na mata masu shekaru 45 na dauke da cutar.
An kuma gano cewa suna kamuwa da Ƙanjamau ne ta hanyar saduwa da juna da kuma yin ta’ammali da miyagun kwayoyin.
A bangaren tarin fuka kuma gidajen yarin dake kudu maso kudu sun ne yawan fursinonin dake dauke da tarin fuka inda adadin yawan su ya kai kashi 71 bisa 100 da kashi 63 bisa 100 a gidajen yarin dake Kudu Maso Gabas.
A karshe jami’in USAID Erasmus Morah ya yi kira ga gwamnatin Najeriya kan samar da magungunan cututtukan ƙanjamau da tarin fuka wa kowa-da–kowa musamman waɗanda ke tsare a gidajen yari.
Mora ya ce yin haka ne kaɗai hanyar da Najeriya za ta bi wajen samun nasara idan har ana so a iya kau da cutar ƙwata-ƙwara a 2030.
Discussion about this post