Zan fito takarar mataimakin shugaban majalisar dattawa ko da APC ba ta yarda ba – Uzor Kalu

0

Sanata Orji Uzor Kalu daga Abia, ya jaddada cewa zai tsaya takarar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ko jam’iyyar APC ta amince, ko ma ba ta yarda ba.

Kalu ya yi wannan furucin ne a lokacin da ake hira da shi a matasayin bakon musamman a gidan talbijin na Channels a yau Alhamis.

Ya ce zai fito takarar ce da kuma yakinin samun nasara, domin tabbatar da cewa Yankin Kudu Maso Gabas ya samu cikakken wakilci a Majalisar Dattawa.

Tsohon gwamnan ya taba yin jam’iyyar PDP, amma a yanzu ya ci zabe ne a karkashin APC.

Ana tuhumar sa da harkallar naira bilyan 7.7 tun a cikin 2007 bayann saukar sa gwamnan jihar Abia, amma har yau ba a kai karshen shari’ar ba.

“Bari na sanar da ku, kai ko da jam’iyyar APC ba ta goyi baya na ba, ko ta ce kada na yi takara, to ni dai sai na fito takarar mataimakin shugaban majalisar dattawa. Zan fito ne domin yankin mu na Kudu maso Gabas ya samu wakilci.

Idan ba a manta ba. Malisar Dattawa da ta sauka a yau Alhamis, dan yankin Kudu maso Gabas ne. Ike Ekweremadu ya yi mataimakin shugaba har tsawon zangon ta, na shekaru hudu.

Shi ne mataimakin Bukola Saraki.

Share.

game da Author