Akalla gidaje 54,197 aka yi wa rajista domin karbar tallafin naira 5,000 kai-tsaye daga Gwamnatin Tarayya a Jihar Zamfara.
Kodinatar Shirin ta Kasa mai suna Temitope Sinkaiye ce ta bayyana haka a Gusau, babban birnin Jihar ranar Juma’a, a lokacin da aka shirya taron yi wa jami’an shirin bitar kwana daya.
Daya daga cikin manyan jami’an shirin ta kasa, Sadiya Abdullah ice ta wakilci Sinkaiye. Ta ce za su rika samun kudin ne a duk wata daga kudaden da gwamnati ke turawa kai-tsaye a asusun ajiyar su na banki.
Sadiya ta ce an zabi Kananan Hukumomin Anka, Bungudu, Birnin-Magaji, Kaura-Namoda, Tsafe da Talata Mafara a matsayin inda za a fara cin moriyar shirin.
Ta ce shirin na daya daga cikin tsare-tsaren tallafawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da shi, kuma ta ke wa talakawa wajen rage musu radadin kuncin rayuwa.
“Za a bayar da naira 5,000 ce, amma kuma za a bayar da na wata biyu a lokaci guda, domin kudin su zamana sun isa wanda aka bai wa ya yi tattalin samun fara ajiye dan wani abu daga ciki domin tattalin dogaro da kai.
Ta ce a yanzu an samu jami’an kula da tura kudaden har su 137 a cikin kananan hukumomin shida da za a fara da su.
Jami’an da suka wakilci gwamnatin Jihar Zamfara sun nuna farin cikin fara wannan shiri a jihar. Sannan kuma sun sha alwashin cewa gwamnatin jihar za ta bada goyon baya da hadin kai wajen ganin an cimma nasarar shirin.
Discussion about this post