Wakilan jam’iyyar PDP da suka bayyana a gaban kotun dake sauraren kararrakin zaben gwamnan Kaduna sun bayyana cewa lallai akwai wurare da dama da ba ayi zabe ba ma a musamman Zariya wanda an gangandane kawai aka yi ta rubuta sakamakon zaben da ba ayi ba.
Wakilan PDP 18 ne suka bayyana a kotu kuma dukkan su sun bayyana cewa tabbas aba ayi zabe aba a wuaren da suka yi aiki.
Yahaya Abubakar wanda wakilin PDP ne a unguwar kwarbai ya ce a mazabar da yayi zabe, tabbas ba a yi zabe ba domin har aka tashi ana ta kai ruwa rana ne da wakilan da ma’aikata amma kawai sai daga baya ya ga wai an rubuto sakamakon zabe a takarda wai har da na mazabar da yake. ” Abin ya daure min kai matuka.
Shi ko Ahmed Babajo cewa yayi kamar yadda yahaya ya fadi, ba a yi zabe a mazabar sa ba amma kuma an hada baki da jami’an INEC an rubuto sakamakon karya aka ce wai abinda aka samu kenan.
Amma kuma Mohammed Dogara, ya fadi cewa lallai an yi zabe a mazabar sa amma kuma ba abinda aka kada bane aka bayyana domin kuwa ko shi da yaga sakamakon da aka ce wai an kada a wannan mazaba sai da ya nemi yanke jiki ya fadi.
Lauyan PDP Elisha Kurah ya bayyana cewa suna nan zasu ci gaba da bayyana shaidu har iya yadda kotun za ta iya saurare. Domin suna da akalla shaidu sama da 680 dake kan layi domin su bada shaidar cewa anyi wa PDP karfa-karfa a zaben gwamnan Kaduna.