ZABEN 2019: INEC ta nemi a kori karar da PDP da Atiku suka shigar a kotu

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta roki Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta kori karar da PDP da dan takarar ta, Atiku Abubakar suka kai kotu.

Atiku da jam’iyyar PDP su na kalubalantar nasarar da INEC ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a kan Atiku, a zaben Shugaban Kasa na 2019.

A cikin wani ba’asi da lauyan INEC mai suna Ustaz Usman ya shigar a kotu, a yau Talata, ta roki kotu ta kori karar da PDP ta shigar, bisa hujjar cewa PDP ba ta hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo a cikin wadanda ta ke kara ba.

Tare da sunan Yemi Osinbajo ne Shugaba Muhammadu Buhari ya samu galabar nasara a zaben a ranar 23 Ga Maris.

Sai dai kuma da ya ke maida martani, babban lauyan PDP mai suna Levi Uzoukwu, ya bayyana rokon da INEC ta yi wa kotu a matsayin wani abu bambarakwai.

Daga nan sais hi kuma ya roki kotu ta kori rokon da INEC ta yi, tare da gargadin ta cewa ta tsaya a wuri daya, ta daina karkata a wani bangare.

Babban Lauyan Buhari, Wale Olanipekun ya goyi bayan rokon da lauyan INEC Usman ya yi, inda ya rika sheka wa kotu ruwan ayoyi daga Kundin Dokokin Najeriya.

Olanipekun ya ce wa kotu ya kamata kotu ta tattauna wannan roko da INEC ta yi, kafin ainihin gundarin shari’ar, kuma kotun ta amince da hakan.

Bayan Shugaban Kwamitin Alkalan Shari’ar, Mohammed Garba da sauran alkali sun gama jin ba’asin Usman lauyan INEC, ya bayyana cewa kotu za ta yanke hukuncin wannan roko da INEC ta yi a nan gaba.

Garba shi ne sabon Shugaban Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa, wanda aka nada, bayan janyewar Shugabar Kotun Daukaka Kara, Zainab Bulkachuwa.

Share.

game da Author