ZABEN 2019: Atiku ya yi daidai da ya maka Buhari a kotu –Jonathan

0

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya yi daidai da ya kalubalanci nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a zabe 2019.

Jonathan ya ce rashin adalci ne karara a rika kwatanta yanayin zaben 2015, wanda shi Jonatahan din ya rungumi kaddara da kuma yadda zaben 2019 ya gudana.

Jonathan ya ce sabubban da suka haifar da dalilin da ya sa ya karbi kaddarar faduwa zabe a 2015, kwata-kwata sun sha bamban da irin yadda zabe ya gudana a 2019, wanda Atiku ya yi takara tare da Buhari.

Zaben 2019 ya wanzu a cikin tashe-tashen hankula da kuma kwamacala da karankatakaliyar satar akwatu, kekketa kuri’u da barazana ga jami’an zabe da masu jefa kuri’a.

Wannan bayani na Jonathan ya na kunshe a cikin wata Mujalla, bugu na Musamman da PREMIUM TIMES ta buga, domin cikar Najeriya shekara 20 da komawa mulkin dimokradiyya, wato 1999 zuwa 2019.

“A lura da cewa a lokacin da na INEC ta shirya zaben 2015, ni ne Shugaban Kasa. Kuma duk da cewa INEC ta cin gashin kan ta, ai dai a karkashin shugaban za a ce ta ke.

“Amma a zaben 2019 shi Atiku ba shi ne shugaban kasa ba. don haka idan shi ko jam’iyyar san a ganin cewa an yi musu rashin adalci, to su na da ‘yancin garzaya kotu.” Inji Jonathan.

Har ila yau, Jonathan ya yi amfani da wannan dama inda ya jinjina wa kan sa wajen kokarin da gwamnatin sa ta yi a bangaren inganta tattalin arziki.

Ya ce duk da dala daya ta kai naira 200 a lokacin sa, amma dai akwai ingantaccen tattalin arzikin kasa.

Duk da cewa akwai sauran tafiya a gaba, Jonathan ya ce da gwamnatin sa ta dore, da tattalin arzkin Najeriya ya kara bunkasa fiye da yadda ake ciki a yanzu.

Share.

game da Author