Jaridar PREMIUM TIMES ta samu yin wannan mashahuriyar tattaunawa da Mohammed Bello Adoke, Ministan Shari’a na lokacin mulkin Goodluck Jonathan, daga 2010 zuwa 2015, a Accra, babban birnin kasar Ghana. Wannan tsakure ne daga cikin hirar da aka yi da shi, domin masu karatun mu su karanta su ji irin kwatakwangwamar tuggu, kutinguila da annamimancin da manyan jami’an gwamnati su ka sha tafkawa a lokacin gwamnatin Jonathan, musamnan kafin saukar sa.
Sannan da yadda Patience Jonathan ta tsaya a gabansa ta surfa masa zagi.
“Gaskiyar magana tabbas Patience Jonathan ta surfa min zagi, saboda na taka rawa sosai wajen kokarin lallashin Goodluck Jonathan da kwantar masa da hankali cewa ya karbi kaddarar faduwa zabe, tun ma kafin a bayyana sakamako.
Saboda mun hango abin da zai iya biyo baya, idan aka samu akasin haka. Ba ni kadai ba ne, don haka babu wanda zai bugin kirji ya ce ya fi wani taka rawa wajen bai wa Jonathan shawarar ya karbi kaddara.
“Ranar 30 Ga Maris, 2015, kwana daya kafin Jonathan ya mika wuyan karbar kaddara ne abin ya faru tsakani na da Patience. Amma a gaskiya ni dai ban ga laifin ta ba, domin ta fito ta amayar da bin da ke cikin zuciyar ta. Kenan ta fi sauran munafukan da suka rika zuwa su na cewa Jonathan wai ni Ministan Shari’ar sa ba na tare da shi.
Munafukai suka rika ce masa wai ni yaron Buhari ne, ina taimaka wa kamfen di Buhari da kudi. To sai ga shi su wadannan munafukan su ne ma suka kewayawa su na taimaka wa Buhari da kudin kamfen, alhalin kuma su na tare da Jonathan, a cikin gwamnatin sa.
Tabbas Patience ta surfa min zagi, amma dalili, a tunanin ta waccan mawuyacinn hali da ake ciki, sun dauka Ministan Shari’a, kuma Antoni Janar na Kasa, wato ni kenan, kamar rayuwar su ko mutuwar ta na ga hannu na. ita ba ta san ni kai na akwai iyakar hurumin da doka ta gindaya min ba. Patience ta surfa min zagi ne a bisa hujjar karairayin da wasu munafukai suka rika zuwa suna sheka mata dangane da ni.
“Ta kira ni shashasha wanda bai san abin da ya ke yi ba. amma fa ku tuna, ai ba shugaban kasa ne ya kira ni haka ba. Na same shi na ce ‘Ranka ya dade kai ka yarda ni sakarai ne kuma shashasha? Kuma ka yarda da abin da ake zuwa ana fada maka dangane da ni? Y a ce a’a bai yarda ba.
“To amma ku fa yi la’akari, ita mace ce, kuma matar shugaban kasa. Babu yadda za a yi ta so mulki ya subuce daga hannun su haka kawai. Maganar gaskiya kenan, shi ya sa ni ban rike ta a zuciya ta ba.
Discussion about this post