Za mu rage yadda ake samun maganin kwari ‘Sniper’ a kasuwanin kasar nan -NAFDAC

0

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta bayyana cewa za ta hada karfi da karfe da wasu hukumomi domin ganin an rage siyar da maganin kwari ‘Sniper’ a kasuwanin kasar nan.

Shugaban hukumar Moji Adeyeye ta bayyana haka kamar yadda gidan jaridar ‘Vanguard’ ya wallafa.

Adeyeye ta ce NAFDAC ta dauki wannan mataki ne ganin yadda mutane musamman matasa ke kwankwadan wannan ruwan magani domin kashe kansu.

” Wani abin tashin hankali da ya zama ruwan dare a tsakanin matasa yanzu shine da zarar sun fusata sai su kwankwadi maganin kwari na ‘SNIPER’ su kashe kansu.

” A kwanakin baya mun samu labarin wani dalibi a jami’ar Nsukka dake jihar Enugu mai suna Chukwemeka Akachi ya kashe kansa bayan ya kwankwadi wannan maganin. Daga nan wasu daliban jami’ar jihar Legas Ayomide da Ajani Danilola sun kashe kansu saboda an zargesu da satan kaya a dakin da suke kwana a jami’ar.

” Shima wani fasto da wata mata ma’aikaciyar banki a jihar Delta mai suna Peace sun kashe kansu ta hanyar kwankwadar wannan ruwan magani.

Adeyeye ta ce duk hakan ya yiwu ne saboda saukin farashi da saukin samu a kasuwanni da wannan magani ke da shi.

” Duk kasuwar da ka shiga a kasar nan za ka samu wannan magani kuma a kan farashin sa bai wuci Naira 200 zuwa 300 ba.

Adeyeye ta ce daga yanzu hukumar su ta amince a canja fasalin wannan magani zuwa roba dake da wuyan budewa ko kuma wanda ake fesawa kamar shaltos.

YADDA AKE AMFANI DA MAGANIN KWARI ‘SNIPER’

Bayanai sun nuna cewa wata kamfanin Najeriya da ta hada gwiwa da kamfanin kasar Swiss ne ke sarrafa wannan magani domin kashe kwari a gonaki.

Bisa ga sharadin amfani da maganin sai an garwaya wannan maganin da ruwa ko kuma da kananzir kafin a yi amfani da shi a gonar sa.

Sai dai kuma a dalilin amincin da wannan maganin ke da shi mutane na amfani da shi a cikin gidajen su domin kashe saro, kyankyasai da sauran kwari a gidajen su.

Wata masaniyar Kwari Fatimah Ahmed ta ce abin takaici ne yadda mutane ke amfani da maganin batare da kiyaye sharuddan maganin ba.

” Misali wasu kan yi amfani da maganin a cikin wake, masara da sauran hatsi sannan wasu kan zubashi a cikin dakinsu domin kashe kwari ba tare da sun rage karfin maganin ba.

” Yin haka na cutar da kiwon lafiyar mutum domin yawan shakar wannan maganin na iya hana mutum numfashi, kawo ciwon ciki,bata fatar jiki sannan yakan iya yin ajalin mutum.

Share.

game da Author