Za a yi zaben kananan hukumomi a jihar Jigawa – Hukumar Zabe na jihar

0

Hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Jigawa (JISIEC) ta bayyana cewa ta kammala shiri tsaf domin gudanar da zaben kananan hukumomi 27 a jihar.

Shugaban JISIEC Muhammed Ahmed ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Dutse ranan Laraba.

Ya ce JISIEC ta tsayar da ranan 29 ga watan Yuni a matsayin ranar da za a gudanar da zaben a jihar.

“ Mun kammala shiri tsaf domin daukar ma’aikatan wucin gadi, kayan zabe, motocin da za su yi jigilan kayan zabe da ma’aikata da kuma sauran su.

“Ina tabbatar wa duk mutane cewa zaben Kananan hukumomi zai gudana a wannan jihar sannan duk wanda shekarun su ya kai na yin zabe su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’un su a wannan rana”.

Share.

game da Author