Za a rika ba masu fama da Kanjamau magani Kyauta a Jihar Ribas

0

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya bayyana cewa daga yanzu duk masu fama da cutar kanjamau za su rika karbar maganin cutar kyauta a jihar.

Wike ya fadi hake ne a lokacin da tawagar hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasar Amurka ta ziyarci gwamnan a fadar gwamnati a Fatakwal.

“ Kasar Amurka za ta tallafa mana da magungunan cutar kyauta inda hakan ya sa za mu daina karban kudade daga hannun masu fama da cutar.

Idan ba a manta ba a watan Maris ne sakamakon binciken da hukumomin NACA da NAIIS suka gudanar ya nuna cewa jihar Ribas na cikin jihohin da suka fi fama da wadanda suka kamu da Kanjamau.

Sakamakon binciken ya kara nuna cewa jihar Akwa-Ibom ce ta fi kowace jiha yawan mutanen dake dauke da cutar sannan sai jihar Benuwai.

Bayan haka jagoran wannan tawaga Tedd Elerbrock ya bayyana cewa sakamakon bincike ya nuna cewa adadin yawan mutanen dake dauke da kanjamau a jihar Ribas ya kai 210,000 wanda daga ciki mutane 40,000 ne kawai ke samun magani kai tsaye.

A dalilin haka Ellerbrock ya ce za su hada hannu da gwamnati domin ganin an dakile yaduwar cutar.

A kwanakin baya ne Hadaddiyar kungiyar masu dauke da cutar kanjamau (NEPWHAN) ta koka kan yadda mamobinta masu dauke da wannan cuta ke biyan har Naira 2000 duk wata domin samun maganin cutar a kasar nan.

Jami’in kungiyar reshen jihar Legas Peter Obialor ne ya koka kan haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.

Obialor yace a dalilin haka da dama daga cikin wadanda ke fama da cutar dake basu iya samun magani.

” Sannan wani abin takaici shine hatta yin gwaji sai mambobin mu sun biya da haka bai kamata ba.

Obialor ya ce a dalilin haka ne yake kira ga gwamnati data gaggauta daukan mataki don hana hakan ci gaba da faruwa ganin cewa hakan na iya kawo koma baya wajen a kokarin da ake yi na kawar da cutar daga nan zuwa shekarar 2030 da gwamnati ke kokarin ganin ya tabbata.

Share.

game da Author