Shugaban hadaddiyar kungiyar fina-finan Hausa (MOPPAN) Kabiru Maikaba ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba dakatar da shiryawa da nuna fina-finan Hausa na soyayya domin a maida hankali kan wasu fina-finan da zasu gyqra tarbiyya da nuna tarihi da al’adun Arewa.
Maikaba ya fadi haka ne da yake hira da BBC Hausa inda ya bayyana cewa kusan kashi 89 bisa 100 na fina-finan da ake yi a Kannywood duk na soyayya ne.
” Meya sa za mu rika yin fina-finan soyayya kawai bayan akwai wasu bangarorin da muke so a rika tabawa.Arewacin Najeriya na da tarihi masu ma’ana da ilmantarwa, me zai sa baza mu rika taba wadannan bangarori ba?
” Nan ba da dadewa ba za mu yi zaben kungiyar MOPPAN, da zaran mun gama za mu zamu maido da hankali kan haka. Zamu rika sanin jigon jigon labarin fim kafin mu amince da shi.Idan kuma muka ga na soyayya ne za mu dakatar da shi sannan za mu ci gaba da daukar wannan mataki har na wani tsawon lokaci.
Maikaba ya kara da cewa za su dawo da yin ire-iren wadannan fina-finai na soyayya ne kawai bayan gamsu da yin fina-finai da suka tabo wasu bangarorin rayuwa da ya kamata fina-finan Hausa suna yi.
Sai dai kuma wasu masu shirya fina-finai sun fara tofa albarkacin bakinsu game da wannan hukunci da MOPPAN ta dauka.
Wani mai koyar da rawa a fina-finan Hausa Ali Ali ya bayyana cewa hana su yin fina -finan Hausa ta soyayya kamar kashe harkar fina-finan Hausa zai yi.
” Na amince cewa ya dace masu shirya fina-finai su rika tabo wasu batuttuwa bayan soyayya amma ka ce kada a yi fim din soyayya hakan bamai yiwuwa bane.”
Hassana Dalhat, fitacciyar mai yin sharhi game da fina-finan Hausa, ta zanta da wakilin PREMIUM TIMES HAUSA inda ta ce lallai akwai ‘yar gajeruwar matsala da za a iya samu idan har za a aiwatar da wannan abu da MOPPAN take shirin yi.
” Tabbas idan MOPPAN ta yi haka za a samu ci gaba wajen shirya fina-finai saidai matsalar da za a iya samu shine mutanen yankin Arewacin kasar nan sun saba ne da fina-finan soyyaya. A dalilin haka zai yi wuya ace wai an iya dakatar dashi farad daya. A dai rika yin kira ga masu shirya fina-finan da su rika shirya wasu da ba lallai na soyayya ba.