Za a fara amfani da sabon katin shaidar yin rigakafin Zazzabin Shawara

0

Ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Yuli za a fara amfani da sabon katin rigakafin shawara a Najeriya.

Darektan harkokin yada labarai na ma’aikatan Boade Akinola ya sanar da haka inda ya kara da cewa a wannan karon an yi katin ne ta yadda na’ura ne kawai zai iya gane ingancin katin.

“Tun a watan Agusta 2017 ne aka shigo da wannan katin sannan an tsara Katin yadda duk kasar da dan Najeriya ya shiga zai karbuwa.

Babban sakataren ma’aikatar Abdulaziz Abdullahi ya bayyana cewa gwamnati ta amince a canja katin nuna shaidan rigakafin cutar ne ganin yadda jabun katin ya kareda kasar nan.

“Sakamakon bincike ya nuna cewa mutane a duk lokacin da suka bukaci fita kasar kan sami wannan katin batare da yin allurar rigakafin ba.

“A dalilin haka ya sa gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta hana wasu ‘yan Najeriya 125 shiga kasar ta a 2012.

SHAWARA

Malaman asibiti sun bayyana cewa akan kamu da zazzabin shawar idan sauron dake dauke da cutar ya ciji mutum sannan mutum kan kamu da cutar a jikin mutumin dake dauke da cutar.

Alamun an kamu da zazzabin. sun hada da zazzabi, amai, ciwon kai, ciwon jiki,gajiya da sauran su.

Sakamakon bincike ya nuna cewa cutar ya sake bullowa a Najeriya 2017 inda tun daga lokacin gwamnati ta dauki matakan dakile yaduwar cutar.

Wadannan matakai kuwa sun hada da yin allurar rigakafi wanda allura daya kan samar wa mutum kariya duk rayuwar sa, yin allurar rigakafi da karban kati a duk lokacin da dan Najeriya zai fita zuwa kasashen waje.

Abdullahi ya bayyana cewa daga ranan daya ga watan Yuli kafin matafiyi ya shigo kasar nan sai an tabbatar yana dauke da katin nuna yin allurar rigakafin cutar.

Ya kuma yi kira ga mutanen kasar nan da suyi kokarin yin alluran ko da baza suti tafiya ba.

Share.

game da Author