Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ranar 12 Ga Yuni wata rana ce da za ta kasance mai muhimmanci ga Najeriya.
Atiku ya ce kamata ya yi ranar ta kasance ranar da ‘yan Najeriya za su rika neman mafita daga halin rayuwar kuncin da suke ciki.
A cikin wata takarda da ya fitar a yau Laraba, Atiku ya ce a wannan rana kamata ya yi ‘yan Najeriya su yi tunani a zuciyar su tare da tambayar kan su, shin ko yau ta fi jiya kuwa?
Ya ce ranar 12 Ga Yuni na da muhimmancin da za a ce ta zarce kawai a kaddamar da ita a matsayin ranar tunawa da dimokradiyya.
“Ranar 12 Ga Yuni ita ce ranar ruhin fafutikar dimokradiyya a Najeriya, kuma kandagarkin jingina rayuwar mu.
Atiku ya ce duk da kokarin da aka yi a baya wajen dawo da dimokradiyya, ya ce a halin yanzu an karkace daga kan bin tafarkin dimokradiyya din idan aka yi la’akari da yadda masu mulki ke yi wa doka karan tsaye da kuma bijire wa umarnin kotu.
Ya ce a fafutikar da aka yi lokacin waki’ar 12 Ga Yuni, an tafi a kan yunkurin kafa ingattaciyar dimokradiyya, ba mulkin karfa-karfa ko maka-karya, irin wanda ake gani a yanzu ba.
Daga nan sai ya ce ba bayyana ranar 12 Ga Yuni matsayin ranar hutu ce abu mafi muhimmanci ba, a wannan lokacin da talaka ke fama da yunwa da fatara.
“Wanda ke tunanin inda zai samu abin da zai ci an jima kadan, wane muhimmanci hutun ranar 12 Ga Yuni ke gare shi? Me zai yi da ranar hutun 12 Ga Yuni, alhali ba a iya kare lafiyar sa da rayuwar sa?
“Ba hutun ranar 12 Ga Yuni ne zai gamsar da ‘yan Najeriya ba, a lokacin da kafafen yada labarai ba su da ‘yancin fadar ra’yin su, babu ‘yancin fadar albarkacin baki da sauran jama’a, kuma ana tauye hakkin ‘yan Najeriya.
Atiku ya ci gaba da cewa a yau duk wani mai fafarniya ko kartar kasa wai shi ya na goyon bayan 12 Ga Yuni, to abin da ya kamata ya yi domin a tabbatar da cewa gaskiya ya ke yi, to ya bi doka, ya daina karya doka kuma ya daina take doka. Sannan kuma ya cika dukkan alkawurran da ya daukar wa al’umma.
Daga nan ya tunatar da irin kyakkyawar niyyar ciyar da kasar nan gaba da ke cikin zuciyar Marigayi MKO Abiola, wanda ya ce su na da kusanci na kut da kut.
Discussion about this post