Jami’an ’yan sandan Jihar Jigawa sun damke wani kasurgumin dan fashin da suke nema ruwa-jallo.
An damke Muhammad Bello, wanda aka fi sani da ‘the governor’ a jiya Talata.
Bello ya ce abokan sa ne ke bakin ciki da ganin-kyashin sa, har suka hada baki da ’yan sanda aka kama shi.
Ya ce abokan sa na nukura da shi ne saboda ya na da farin jini ga ’yan mata, kowace sai shi ta ke so.
Bello ya ce abokan sa suka shirya masa tuggun sharrin fashi domin kawai ‘yan sanda su kama shi.
An kama shi a Zaria a lokacin da ya ke gudun buya. Dama kuma sunan sa na daga cikin manyan rikakkun ’yan fashin da ake nema a jihar Jigawa.
Sai dai kuma ya ce farin jinin da ya ke da shi a wajen mata ne ya janyo masa shiga cikin wannan musifa.
“Duk kasuwar da na shiga ko garin da na je, sai ’yan mata su yi ta nuna min so, ko da kuma su na tare da samarin su ne. sau da yawa ma su ke fara yi min magana ko da ni ban yi musu ba.”
“Dalilin da ya sa kenan wasu abokai na da ke yankin mu masu kishi saboda ina kashe musu kasuwar-’yan mata kuma su na jin haushin irin rayuwa ta suka ce wa ‘yan sanda wai ni dan fashi da makami ne.
“Amma babu wani abu, kawai don ’yan mata sun fi so na ne a kan su.” Inji Bello.
Yadda muka kama Bello
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Jigawa Bala Senchi, ya karyata Muhammad Bello dan shekara 25, mazaunin kauyen Jiba da ke cikin Karamar Hukumar Dutse.
Ya ce Jami’an Operaion Puff Adder ne suka kama shi a cikin garin Dutse.
Ya ce an sha kokarin neman kafa shi amma ya na zillewa, har sai ranar Talata da dubun sa ta cika.
“Ya shirya fashi da makami sau da dama a yankin Dutse zuwa Birnin Kudu, kuma ya na hada baki da batagari wajen aiwatar da aika-aikar sa.”
Jami’ai sun ce “shi ne ya ja ‘yan fashin da suka kai wa Dan’azumi Yusuf hari a kauyen Madobi.”
Senche ya kara da cewa “cikin 2017, wanda ake zargin ya hada baki da wasu inda suka yi amfani da bindigar gargajiya suka yi wa wani dan achaba fashi a kauyen Kafin Lemo, cikin Karamar Hukumar Takai ta Jihar Kano.”
“Wanda ake zargin ya kware sosai wajen yi wa masu babura fashi da kuma kwace dabbobi. Kwanan nan ya saci shanu biyu da awaki hudu a cikin wani daji kusa da kauyen Waza cikin Karamar Hukumar Dutse, sannan ya saida daya daga cikin su a kan kudi naira 55,000 ga wani Sarkin-Fawa mai suna Danjummai.
“Danjumai ya shiga hannun jami’an tsaro, inda ya shaida musu cewa ya sayi shanu biyu a hannun Muhammad Bello a kan kudi naira 115,000.” Inji Kwanishinan ‘Yan sanda Senchi.