Yayin da kamfanin jiragen saman Arik Air, mallakar Joseph Arumemi-Ikhide ya hadiyi bashin sama da naira bilyan 100, har ta kai gwamnatin tarayya ta karbi gudanarwar Arik Air daga hannun sa, PREMIUM TIMES ta binciko cewa Arumemi ya mallaki tulin dukiya da dimbin kadarorin da ko Dankaruna sai ya yi mamakin yawan ta.
TULIN BASHIN DA AKE BIN ARIK AIR
Daga cikin bashin da ya cika wa Arik Air ciki fal, har ya kumbura, akwai wata zunzurutun naira bilyan 135 da Hukumar Kula da Kadarori ta Najeriya ke nema daga kamfanin, wadda hakan ta sa tilas AMCON ta bi ta karkashin gwamnatin tarayya aka karbe ragamar tafiyar da Arik Air a cikin Fabrairu, 2017.
An kuma kori dukkan jami’an gudanarwar kamfanin aka nada sabbi da ke tafiyar da Arik, kamfanin zirga-zirgar jiragen sama mafi girma a kasar nan.
Watanni biyu kacal bayan da gwamnatin tarayya ta karbe Arik Air, sai aka gano cewa ashe tulin bashin da ake bin kamfanin sun zarce yadda aka yi tunani daga farko.
Manajan da gwamnatin tarayya ta nada wa Arik, Oluseye Opasanya, ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos cewa kudin da ake bin Arik bashi za su kai naira bilyan 375.
Opasanya ya kara da cewa bayan ya karbi ragamar gudanarwar Arik, an rika kawo masa bayanan wasu basussuka da aka rika neman Arik ya biya. Daga ciki inji shi akwai: Wata fam milyan 31 da jiragen kanikancin jirage na Lufthansa Technik Group ke bi. Sai wata dala milyan 6.5 da hukumar kula da sararin samaniya ta Afrika ta Yamma ke bin Arik bashi. Akwai kuma naira milyan 418.89 kudaden inshora da ake bin Arik Air. Sannan kuma Arik Air ya ci bashin naira bilyan 24.347 a bankin Access da Zenith.
TULIN BASHI BA ADADI
Sauran masu bin Arik Air bashi sun hada da Amades Marketing Nigeria mai bin naira milyan 632.49, wasu bashi na naira bilyan 2 daga bankuna, Hukumar Kula da Filayen Jirage na bin Arik Air bashin naira bilyan 11.21 akwai kuma dala milyan 942.14 da FAAN ke bin Arik Air.
Akwai sauran tulin bashin da ake bin Arik Air, wadanda ba sai PREMIUM TIMES HAUSA ta jero su a nan ba. Amma duk ta na da kwafen kididdigar kudaden.
YADDA ARIK AIR YA RIKA KARYA DOKOKIN NAJERIYA
Arik Air ya karya Dokar Fansho ta Sashe na 4 ta 2014, inda ya daina ajiye kudaden fanshon ma’aikatan sa da rika cirewa daga cikin allbashin su. Sannan kuma ya rika kin bayar da kashi 10 bisa 100 daga aljihun sa, a matsayin gudummawar fanshon na ma’aikatan sa.
Akalla an shafe watanni 65, tun daga 2010 har zuwa 2016 Arik Air bai tara ko kwandala daga cikin kudaden fanshon ma’aikatan sa ba.
Kudaden fanshon da ake bin Arik bashi sun doshi naira bilyan 4.59.
Arumemi, Attajiri Mai Dukiya Malala-gashin-tinkiya
Bayanan tulin dukiyar da Joseph Arumemi ya mallaka, wanda PREMIUM TIMES ta ci karo da su, tun wadanda aka yi lissafin kididdiga a cikin 2014 ne. Wato shekaru uku kafin AMCON ta karbi ragamar tafiyar da Arik Air daga hannun sa.
Sai dai kuma ba a sani ba daga wancan lokacin zuwa yanzu, shin raguwa dukiyar ta yi ko kuwa karuwa ta yi.
Cikin watan Satumba, 2011 an kiyasta darajar rukunin wasu kamfanonin sa, Nigerian Property Portfolio a kan kudi dala milyan 116.
Akwai Arik Air Center, wasu kadarorin sa da ake fa Filin Saukar Jirage na Murtala Mohammed da ke Lagos, an kiyasta kudin su a cikin 2012 cewa za su kai dala milyan 963.17.
Sai kuma kamfanin Rockson Engineering da aka kiyasta a kan dala milyan 767.1 a cikin Disamba, 2012.
Wasu kadarorin sa da ke Ingila, ciki har da Ojemai Properties da Overbury Properties su kuma a kiyasin Juli, 2013 aka ce za su kai dala milyan 44.
Kididdigar da kamfanin kididdigar kadarori da tulin dukiya mai suna Deliotte yayi cikin Mayu, 2013, ya kiyasta darajar kamfanin Arik Air ta kai dala bilyan 1.04.
Yayin da jimillar kadarorin Arumemi aka kiyasta sun kai dala bilyan 3. An kuma kididdige bashin da aka bin sa zai kai dala milyan 514.8
TULIN HANNAYEN JARIN ARUMEMI A BAKUNA
Ya zuwa cikin Oktoba, 2014, an kiyasta darajar hannayen jarin sa a bankuna daban-daban za su kai nair bilyan 8.36, kwatankwacin dala milyan 51.6 kenan.
Wasu bakunan da ya ke da hannayen jari sun gada da Zenith, Fedility, First Bank da kuma bankin Keystone.
PREMIUM TIMES ta tura masa sakon neman jin ta bakin sa a lambar wayar sa da kuma i-mel, amma har lokacin da aka kammala rubuta labarin, bai maido amsa ba.