Mata da dama sun koka cewa babban dalilin da ya sa ake samun matsala a wajen iya samun nasarar yin na’am da amfani da magungunar tazarar iyale shine yadda wasu mazan ke yi wa abin kunnin karfe, wato bau yarda da matan su su yi amfani da ire-iren wadannan magunguna.
Halemma Yousef uwar ‘ya’ya biyar ta bayyana cewa za ta so ace ta daina haihuwa yanzu amma tsoron bacin ran mijinta shine babban matsalar da ya sa bata ma waiwayi hakan ba.
Haleema ta ce suna zama ne tare da mijinta a Abuja a daki daya da ya’yan su. Saboda tsadar rayuwa dole na ke dan yin sana’ar hannu da ya hada da kitso, yin kunun Zaki da alala domin samun na kashewa.
Asibiti sun horas da mu yadda za mu iya bada tazarar iyali amma ba zan iya amfani dashi ba saboda mijina baya so. A dalilin haka dole na hakura na koma ina yin abin aboye ne kuma ma da na gargajiya na ke yi, inda ko da ya gani ina sha ba zai gane cewa maganin kayyade iyali bane.
Alias Umar da Amina Umar matan mutum daya kuma ‘yan gudun hijira daga jihar Barno sun bayyana cewa amfani da dabarun bada tazaran iyali ya zama musu dole ganin yadda suke samun matsala wajen haihuwa da yawan mace macen ‘ya’yan su da suke fama da shi.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne cibiyar ‘Development Research and Project Centre (dRPC)’ ta shirya taro domin tattauna hanyoyin bunkasa amfani da dabarun bada tazarar iyali a Najeriya.
Jami’in dRPC Emmanuel Abanida ya bayyana cewa har yanzu dai mutane musamman mata na gudun amfani da dabarun bada tazarar iyali a Najeriya.
Abanida ya ce bincike ya nuna cewa kashi 11 bisa 100 na mata a Najeriya ne kacal ke amfani da dabarun.
Ya ce kamata ya yi mutane su gane cewa amfani da dabarar bada tazaran iyali hanya ce dake taimakawa wajen inganta kiwon lafiyar mace da na yara.
” Ya zama dole fannin kiwon lafiya tare da masu fada a ji a fanin su zage damtse wajen ganin an wayar da kan mutane game da mahimmancin amfani da dabarun bada tazaran iyali.
Amfani 4 da dabarun tazaran iyali ke da shi.
1. Yana inganta kiwon lafiya mace ganin cewa dabaran tazaran iyali hutu ne da mata ke samu kafin su sake haihuwa.
2. Inganta kiwon lafiyar yara saboda mace za ta sami lokacin kula da danta yadda ya kamata kafin ta sake w2ani haihuwan.
3. Hana yawan mace macen mata da yara kanana.
4. Amfani da dabaran tazaran iyali na han