Yadda kasahen Afrika ta yamma za su iya kawo karshen Ta’addanci – Buhari

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari,wadda shine tsohon shugaban kungiyar raya kashashen yankin Afrika Ta Yamma ya bayyan cewa dole sai kasashen wannan kungiya sun tashi tsaye matuka kafin su iya kau da matsalar tsaro da ya addabi kasashen nasu.

Buhari ya bayyana haka ne a jawabin da yayi wa shugabannin kasashen yankin a taron ta a Abuja, Najeriya.

Buhari ya sauka daga shugabancin wannan kungiya a ranar Asabar inda aka zabi shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issofou a matsayin sabon shugaban kungiyar ECOWAS din.

” Kasashen mu sun fada cikin halin kakanikayi saboda hare-hare da ayyukan yan ta’adda. Hakan yasa tsaro ga mutanen kasashen mu ya karanta. Sai dai kuma mun samu nasarori da dama a yaki da ayyukan ‘yan ta’adda da muke yi a kashen mu.

” Babban abinda za mu fi maida hankali akai shine tsaurara matakan tsaro a kasahen mu. Sannan kuma da kawo karshe takauci ga mutanen da samar da ci gaba.

Share.

game da Author