An haifi sabon Shugaban NNPC Mele Kyari ranar 8 ga watan Janairu, 1965 kuma ya kammala digirin sa na farko a Jami’ar Maiduguri cikin 1987.
Ya karanci Nazarin Albarkatu da Kimiyyar Karkashin Kasa.
Kyari kwararren masani harkokin man fetur ne da ya shafe shekeru 32 ya na aikin harkokin danyen mai da albarkatun kasa.
Ya yi aiki a bangarori da dama, kuma ayyukan sa sun rika yin tasiri a sauran bangarorin NNPC.
“Ya taka rawa wajen samar da ingantaccen sauyin ciniki da hada-hadar danyen man fetur, ta hanyar gudanar da harkokin tafiyar da kasuwancin a bisa ka’ida, ba tare da kumbiya-kumbiya ba.”
Ya yi aikin bautar kasa (NYSC) a Hukumar Inganta Abinci da Titinan Raya Karkaka (DFRRI), a cikin 1987 zuwa 1988.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Mele Kyari a matsayin sabon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC).
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na NNPC, Ndu UJghamadu ya fitar, ya ce Buhari ya kara da nada wasu sabbin Manyan Jami’an Ayyukan NNPC su bakwai.
Kyari shi ne ya gaji tsohon shugaban kamfanin NNPC, Maikanti Baru.
Kafin nada Kyari, shi ne Babban Janar Manaja mai kula da Bangaren Kasuwaci da Cinikin Danyen Mai.
Kuma tun daga watan Mayu 2018 aka kara masa matsayi inda ya shi ne Wakilin Najeriya a Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC).
Sauran Manyan Jami’an NNPC bakwai da aka nada sun hada:
1. Roland Onoriode Ewubare (Maso-Kudu)
2. Mustapha Yinusa Yakubu (Arewa Ta Tsakiya)
3. Yusuf Usman (Arewa Maso Gabas)
4. Lawrencia Nwadiabuwa Ndupu (Kudu Maso Gabas)
5. Umar Isa Ajiya (Arewa Maso Yamma)
6. Adeyemi Adetunji (Kudu Maso Yamma)
7. Farouk Garba Said (North Yamma)
Ughamadu ya shaida cewa Sugaban Kamfanin NNPC mai barin gado, Maikati Baru ya taya sabbin wadanda aka nada din fatan alheri.