USAID ta ware dala miliyan 225 domin tallafa wa fannin kiwon lafiyar jihohi biyar a Najeriya

0

Hukumar USAID ta ware dala miliyan 225 domin tallafa wa fannin kiwon lafiyar jihohi biyar a kasar nan.

Jami’in USAID Stephen Haykin ya sanar da haka a wani taro da suka yi a Abuja ranar Talata.

Haykin ya ce USAID za ta fara inganta fannin kiwon lafiyar jihohi uku daga cikin biyar a kasar nan.

Wadannan jihohi kuwa sun hada da Bauchi,Kebbi da Sokoto.

“USAID za ta tallafa wa wadannan jihohin ne ganin yadda sakamakon bincike ya nuna cewa mutanen wadannan jihohin na fama da matsalolin rashin kiwon lafiya na gari.

“Za mu fi bada karfi wajen inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana a wadannan jihohi domin rage yawan mace macen mata da yara kanana.

“Yin allurar rigakafi, awon ciki, samar da kula wa mata yayin da suke da ciki da bayan sun haihu, kawar da cutar hakarkari, zazzabin cizon sauro da dai sauransu.

Haykin yace bayan sun kammala da wadannan jihohi za su zabo wasu jihohi biyu kuma domin ci gaba da wannan aiki.

Idan ba a manta ba Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya bayyana cewa rashin kwararrun ma’aikata, rashin samar da ingantattun kayan aiki a asibitoci musamman a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na daga cikin matsalolin dake hana Nahiyar Afrika iya kawo karshen yawan mace-macen yara kananan da mata a kasashen su.

Bisa ga sakamakon binciken da UNICEF ta gudanar ya nuna cewa rashin yawan ma’aikatan kiwon lafiya a Najeriya ya yi wa fannin kiwon lafiyar kasar Najeriya katutu inda a duk shekara mata 576 da yara kananan ‘yan kasa da shekara biyar 37 ne ke mutuwa.

Sakamakon ya kuma nuna cewa an fi samun mafi yawan mace-macen yara kanana da mata a yankin arewacin kasar a dalilin fama da matsanancin talauci da suke yi.

Bayan haka kungiyar likitocin hakora na kasa (MDCN) ta bayyana cewa adadin yawan likitocin da suka yi rajista da kungiyar su a 2017 sun kai 42,845 wanda daga ciki 39,912 ne suke kwararru.

A lisaffe bisa ga hukumar kidaya ta kasa adadin yawan mutanen Najeriya a 2016 sun kai miliyan 193.4 sannan idan aka kwatanta yawan da yawan likitocin dake kasar nan za a gane cewa likita daya na duba akalla marasa lafiya 4,845 a Najeriya.

A karshe UNICEF ta yi kira ga gwamnatin Najeriya kan yin amfani da wannan sakamakon bincike wajen samar da mafita daga wannan matsala da ake fama da.

Haka na nufin daukar ma’aikata da inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya.

Share.

game da Author