Ummi Zeezee ta saki sabon waka

0

Fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Kannywood Ummi Zeezee ta shiga sahun mawakan Kannywood inda ta saki sabon wakar ta mai suna Janglover.

Zeezee ta saka wani sashe na wakar a shafinta na Instagram inda tace a saurareta nan ba da dadewa ba.

Masoya sun fantsama shafinta inda suka rika yi mata barka da da wannan kokari da kuma fatan alkhairi.

” Ummi ta yi namijin kokari sannan gogayya da zata yi da mawaka kamar su Adam Zango, M Sheriff da sauran su. Wannan shine karo na farko da mace zata nuna irin wannan hazaka a farfajiyar Kannywood.” Inji Hauwa.

Share.

game da Author