TULIN MAKAMAI: Gwamnoni sun ce wa Amosun ‘kowa ya debo da zafi’, bakin sa

0

Gwamnoni a fadin kasar nan sun maida wa tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun aniyar sa, bayan ya yi furucin cewa ai gwamnoni kan gina manyan rumbunan ajiyar makamai a Gidan Gwamnati.

Amosun ya yi wannan zargin ne a ranar Talata, a lokacin da ya ke kokarin sabule rigar alhakin boye tulin makamai a fadar Gidan Gwamnatin Jihar Ogun, wanda PREMIUM TIMES ta fallasa ya yi a lokacin da ya na gwamna.

Tulin makaman wadanda ya sayo da kudin gwamnati a asirce, kuma ya kimshe a asirce ba tare da sanin jami’an tsaro da sauran hukumomin tsaro ba, babban laifi ne, kuma karya dokar safarar makamai ce ta kara.

Manyan jami’an tsaro na Najeriya sun cika da mamakin yadda Amosun ya shigo da makaman ta haramtacciyar hanya da kuma tababar abin da aka yi niyyar yi da su.

Martanin Gwamnoni 20 ga Amosun

Tsakanin Laraba da kuma jiya Alhamis, PREMIUM TIMES ta samu jin ta bakin ra’ayoyin Gidajen Gwamnati 20 a fadin kasar nan, domin jin martanin su bayan Amosun ya ce ana boye makamai a Gidajen Gwamnati.

A yankin Kudu maso Yamma, an ji na Jihohin Ondo, Osun, Lagos, Oyo, Ekiti da Ogun, inda dukkan su suka karyata Amosun suka ce ba su taba sayo makamai a asirce kuma suka boye a asirce kamar yadda Amosun ya ce ana yi ba. Sun ce wannan duk ba ya cikin ayyukan da doka ta wajibta ta gwamnoni.

Mu dai ba ma irin wannan hada-hadar a Jihar Ondo

“Mu dai ba ma irin wannan hada-hadar a Jihar Ondo. Gwamnan Jihar mu ba mai irin wannan makahon ciniki ba ne, domin ba ya cikin abin da aka zabe shi ake kuma so ya yi. Kai mu dai a jihar mu ba mu bukatar cinikin makamai a sarari ko a boye ma.” Haka Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Yemi Olowolabi, ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Yayin da Jihar Ekiti ta yi mamakin irin wannan rumbun ajiyar makamai da ake magana, ta ce ai ba yaki ta ke yi ba, ballantana ta tanadi makamai. Don haka ba aikin gwamna ba ne sayo makamai har ya gina musu rumbun ajiya a cikin Gidan Gwamnati.

Ba mu da Bindiga ko guda daya, inji gwamnatin Oyo

Ita ma jihar Oyo cewa ta yi ba ta da ko bingida guda daya. Bindiga dai ta hukumar tsaro ce ba ta gwamnatin Jiha ba.

Jihar Oyo ta ce harkar tsaro gwamnan jihar ga jami’an tsaro ya ke mika batun.

Jihohin Osun da Lagos ma duk sun karyata Amosun, sun tabbatar da cewa ba su taba ajiye ko kwafsar harsasai a cikin Gidan Gwamnati ba. Kuma ba su taba gina rumbun ajiyar makamai ba.

Wannan ai babbar wauta ce, Inji Gwamnatin Akwa Ibom

Ekerete Udoh, Kakakin Gwamnan Jihar Akwa Ibom, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa kamar yadda ya ke babbar wauta a yi wannan tambayar, haka ma babbar wauta ce a ce jiha mai takama da zaman afiya da kwanciyar hankali tare da zamantakewar lumana kamar Akwa Ibom, har ma a yi tunanin gwamnatin jihar za ta gina rumbun ajiyar makamai a asirce kuma a cikin Gidan Gwamnati. To me za a yi da da su?

“To mu dai Gwamna Udom Emmanuel ayyukan raya al’ummar jihar ya sa a gaba, ba dillancin makamai ya ke yi ba, kuma ba ya boye makami ko na kyarta ashana a Gidan Gwamnati.”

Gwamnatin Bayelsa ta fusata da Amosun

Kakakin Gwamnan Jihar Bayelsa ya nuna rashin jin dadin yadda tsohon gwamnan Jihar Ogun Ibikunle Amosun ya ce gwamnoni ma su na boye makamai a cikin Gidan Gwamnati.

Ya ce wannan ba gaskiya ba ne, domin dai ko bindigar toka ba a ajiyewa a Gidan Gwamnatin Bayelsa.

“To wai me gwamna zai yi da bindiga a cikin Gidan Gwamnati? Aikin sa ne ajiyar makamai? Ina Hukumomin ’Yan Sanda da sauran wadanda hakkin kula da makamai ke a hannun su?

Babu ruwan El-Rufai da Kimshe Makamai

Jihohin Delta, Edo, Ebonyi, Barno, Yobe da Kaduna duk sun nesanta kan su da ikirarin da Amosun ya yi.

Kakakin Gwamnan Kaduna, Samuel Aruwan ya ce babu ruwan gwamnatin jihar da kimshe makamai.

Ya yi karin hasken cewa idan gwamnatin jihar ta sayo motoci ko babura domin bayarwa gudummawa ga jami’an tsaro wajen gudanar da sintiri, to su na damka musu ne kai-tsaye kawai.

Haka Kano da Benuwai da sauran Jihohi duk sun karyata Amosun.

Ya ce rashin tunani ne wasu su ce wai Boko Haram ajanda ce a kan Kiristocin Najeriya, domin Boko Haram sun ma fi kashe Musulmai sosai fiye da Kirstoci.

Ya ce amma wannan gwamnati ta taka rawa sosai wajen dakile Boko Haram sosai da sosai.

Share.

game da Author