Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle, ya nada Tsohon Ministan Harkokin Kudade, Bashir Yuguda a matsayin Mashawarci na Musamman.
Yuguda wanda kuma ya taba yin jakadan Najeriya, an nada shi ne tare da wasu mashawartan su shida, kamar yadda wata sanarwa daga Babban Sakataren, Ibrahim Sulaiman da ke aiki a karkashin ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfana ta nuna.
Sauran wadanda aka nada sun hada da: Sakataren Gwamnatin Jiha, Abubakar Dauran, Babban Mashawarci a Harkokin Tsaro, Ibarahim Bello da kuma Babban Jami’i mai kula harkokin kakafin yada labarai na zamani, wato soshiyal midiya.
Sanarwar wadda aka fitar tun a ranar Juma’a, ta ce nade-naden sun fara nan taka a lokacin da aka yi sanarwar nadin na su.
Matawalle ya zama gwamna bayan da Kotun Koli ta jaddada hukuncin Kotun Daukaka Kara, wanda ya soke nasarar da APC ta yi a zabukan jihar Zamfara.
An bai wa PDP nasarar a matsayin ta wadda ta zo ta biyu.