Mataimakin shugaban jam’iyyar APC ta kasa shiyyar Arewa, Lawal Shu’aibu ya fadi cewa ba zai bayyana a gaban kwamitin jam’iyyar APC da ta bukaci ya zo gabanta ba.
Idan ba a manta ba a Kwanakin baya ne Lawal shu’aibu ya yi kira ga shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole da ya sauka daga kujerar shugabancin jam’iyyar.
Ya ce Oshiomhole na da hannu a badakalar rasa jihar Zamfara da APC tayi.
Ya ce idan ko ba haka ba shi Oshiomhole din zai yi watsa-watsa da jam’iyyar.
A bisa wadannan kalamai da Lawal ya yi ne jam’iyyar ta nada kwamiti domin ya zo gabanta ya fadi dalilan da ya sa jefi shugaban jam’iyyar da munanan kalamai.
Lawal ya ce ko nada wannan kwamiti da akayi ba a bi dokar jam’iyyar ba.
” Doka ba ta ba jam’iyyar da shi kansa shugabanta zai jagoranci zaman da aka ce wai an nada domin ta bincike ni.
” Ba zai taba yiwu ba ace wai sune za su saurare ni. Bayan haka kuma ni fa ban yi wani da ya saba wa dokar jam’iyya ba.
” Yanzu dai ina so in sanar wa duniya da ita kanta jam’iyyar cewa ba zan bayyana a gaban wannan kwamiti ba.” Haka Lawal ya ce.