Sojojin sun lallasa masu zanga-zanga da dorina a Jihar Barno

0

A Safiyar Alhamis ne ‘yan gudun hijiran dake samun mafaka a sansanin dake titin Gubio a garin Maiduguri jihar Barno suka fito tituna domin yin zanga-zanga da nuna damuwar su game da tsananin yunwa da suke fama da shi a sansanin.

A daidai suna tattaki a titin da ya biyo dasu barikin sojoji dake Maimalari. Suna isa wannan wuri sai sojojin suka han su wucewa suka fatattake su.

Da masu zanga-zangar suka matsa sai sun bi ta gaban wannan bariki sai sojoji suka tsiki iatatuwa da dorina suka rika jibgan su suna kora su.

Wani mazaunin sansanin Modu Muhammed ya bayyana wa manema labarai cewa watan su biyu rabon da ma’aikatan sansanin su garzayo su bamu abinci.

“ Dama wata kungiya mai zaman kanta ne ke zuwa sansanin tana raba mana abinci amma hankalin kowa ya tashi a lokacin da kungiyar ta sanar cewa daga yanzu ba za ta sake zuwa sansanin ba saboda ta kammala rabon abinci da take da shi.

Bayanai sun nuna cewa mazauna sansanin ‘yan gudun hijira a jihar sun dade suna kukan yunwan da ma’aikatan sansanin ke barin su da shi.

A dalilin yunwa da neman mafita mazauna sansanin suka gudanar da zanga-zanga a watan Maris 2018 da wani a watan Fabrairu 2019.

Share.

game da Author