Rundunar sojojin Najeriya ta sanar a safiyar Asabar cewa mayakanta na hadin guiwa da kasar Chadi sun kashe mayakan Boko Haram 48 sannan sun kwato motoci da kayan yaki da dama.
Kamar yadda sanarwar ya bayyana, dakarun sun farwa kauyen Kauwa-Baga-Doron inda maboyar sauran burbudin ‘yan Boko Haram ke suka yi musu diran mikiya, suka rika yi musu luguden wuta ta sama da kasa.
Rundunar ta ce wani sojan Chadi daya ya rasa ransa sannan wasu kuma 12 sun jikkita.
Ciki 12 da aka bayyana bamu san ko sojojin Najeriya guda nawa bane suka jikkita a wannan fafatawa ba.