Sojoji sun kashe ’yan bindiga 15 a Zamfara

0

Sojojin Operation Hadarin Daji sun bayyana kashe mahara 15 wadanda ke addabar kauyukan Dansadau da kewaye a jihar Zamfara.

Wannan ya zo ne lokaci kadan bayan da sojoji suka bada nasarar kashe wasu mahara 29 a wata taho-mu-gama da aka yi yankin Moriki a cikin jihar ta Zamafara.

Laftar Ayobami Orisan ne ya bayyana haka, kuma shi ne kakakin yada labarai na rundunar mai rikon kwarya.

Ya ce an yi wa maharan takakka har mabuyar su da ke cikin dajin Madada a karkashin yankin Dansadau cikin Gundumar Magami a Karamar Hukumar Maru.

Sanarwar ta ce da farko ‘yan bindigar sun fara nuna tirjiya, amma sai aka yi musu kwaf-daya, aka fatattake su kawai.

Ya ce baya ga wadanda aka kashe, wasu sun gudu da raunukan harbin bindiga a jikin su.

“Sojoji sun kashe 15 daga cikin su, kuma suka kone dukkan sansanonin su da ke cikin dajin.”

Sai dai kuma ya ce soja daya ya rasa ran sa, sannan kuma wani dan sintirin bijilante ya samu rauni.

“Har ila yau, a kauyukan Wanke da Kanoma cikin Karamar Hukumar Maru, sojoji sun kwato kimanin shanu 100 daga hannun barayin shanu, wadanda suka sace a yankin Kanoma.

“Yayin da barayin shanun suka hangi sojoji, sai suka tsere suka gudu, bayan sun fara shan harbi. Sannan an kwato shanu 14 a Faru wajen Tungar Hako wadanda mahara suka gudu suka bari.”

Share.

game da Author