Siyasar Daukar Fansa, Tasono, Tsula Da Tunkuza Ba Tayi Kama Da Garin Kano Ba, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Kano ta dabo, tumbin giwa, yaro ko da mai kazo an fika. Wannan shine kirarin Kano a bakin Kanawa.

Garin Kano ya rayu shekaru da yawa, saboda fara samun dan adam ya rayu a garin ta fara ne tun lokacin tsohuwar duniya.

Allah ya ba wa Kano girman tarihi da albarka, don har yanzu babu wata masaniyar adadin shekarun Dutsen Dala (Red sand).

Misali, bincike ya nuna cewa, samun sassan jikin Gwauro da matarsa Dala wadanda suka fara zama a Kano ya kai kusan shekaru dubu sha hudu (14,000 years). Daidai da shekarun ko wani irin ‘civilization’ a duniya.

Bayan mutuwarsu ne, sannan aka samu shigowar maguzawa masu mafarauta daga Sudan.

Hakan ne ma yasa aka samu ‘sedentary communities’ da yawa akan dutsen Goron dutse, Dala, Fanisau, Magwan da sauransu.

Misali, duk wanda ya kalli dutsen Dala ya san babu irin wannan jar kasar (Red sand) a birnin Hausa, masana sun bayyana cewa zai iya kasancewa an ginata ne kamar yadda aka gina masarautar tsohuwar misra (Ancient Egypt).

Mai karantu, ka karanta shafi 98 zuwa 110 a cikin littafin da “Research & Documentation Directorate” Kano ta wallafa a 2010, mai suna ‘Kano Millennium, 1,000 Years In History’. Insha Allah zaka samu karin bayani akan abin da na fada.

Tarbiya da son neman ilimin Kanawa ne yasa Abdullahi Ibn Fodio (Abdullahi Gwandu) ya zauna a garin Kano bayan a baya ya yanke shawarar yin hijra zuwa Makka saboda mutanen gundumarsa sun ki addini.

Ka karanta wancen littafin da na baka hujja dashi a baya.

Saidai abin mamaki, duk irin wannan girman tarihi da tarbiya da garin yake dashi suna kan hanyar lalacewa. Musamman yadda masu rike da mukaman siyasa suka koma yin siyasar da zata rushe mutuncin garin.

Yau mun samu kanmu a cikin siyasar daukar fansa, gaba, zage-zage, tumasanci, gidadanci, rashin kan-gado da sauransu. Babu wanda yafi karfin zagi a Kano yanzu, ko ma waye.

Malaman addinin musulunci a zage, masarauta a zage, attajirai da talakawa a zage, balle kuma ‘yan siyasa da zaginsu ya zama sana’a, har biyan wasu ake yi su zagesu.

Dole matasa suyi ta zage-zage a dandalin sada zumunta da ko ina ma, saboda shine abin da jagororinsu suka koya musu tunda sun hanasu ilimi da sana’a.

Shugabanninmu sun zama daga TSULA, sai TUNKUZA, sai TASONO da sauran sunayen banza.

Kuma fa masu yin hakan sune masu rike da siyasar jihar, abun mamaki duk sun haura shekara 60.

Gaskiya duke mutumin bai baka ilimi ba, burinsa ka rayu cikin qasqanci da bauta.

Saboda rashin fahimta, sai kaji wasu suna cewa wai hakan shine asalin siyasar Kano. Ta ina?

Idan ma haka ne, to ai ya zama irin aikin jahiliyar farko. Shine, an samar damu a cikin kuskure kuma mun ce ba zamu canza daga kuskuren iyaye da kakanninmu ba.

Ko ‘yan siyasar baya idan zasu iya dawowa sai sun yi Allah-wadai da siyasar yanzu.

Allah ya jikan Malam Abubakar Rimi, ai a karshe yayi kuka da salon siyasar da ake yi kafin ya mutu.

Dole sai an ajje siyasar kauyenci, an dauki ta wayewa da cigaba don mu gadarwa da ‘yan baya abun arzikin da su Sardauna suka gadar mana.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author