Hayaniya ta kaure a Zauren Majalisar Dattawa yayin da Magatakardar Majalisar Dattawa ya bayyana cewa za a yi zaben shugabanni a asirce ne, ba a bayyane ba.
Mohammed Sani-Omolori, ya bayyana cewa za a yi amfani da irin tsarin da aka bi aka zabi shugabanninmajalisa a 2015.
Wannan tsari da 2015 dai ya bada fifiko ne cewa a yi zaben shugabannin majalisar dattawa a asirce.
Sai dai kuma a jiya Babbar Kotun Abuja ta yanke hukuncin cewa a yi zaben kiri-kiri, kamar yada tsarin 2011 ya jaddada.
An yi ta hayaniya a majalisa har tsawon minti 10, inda sanatocin da ke goyon bayan kowane bangare ke nuna inda hankalin sa a fi karkata.
A yanzu haka dai ana can ana jefa kuri’a a Majalisar Dattawa, domin zaben wanda zai zama Shugaban Majalisa da kuma sauran mukamai.
Sani Omolori na kiran sunayen sanatoci daya bayan daya domin kowane ya je ya jefa kuri’ar sa.
Sanata Ahmed Lawan shi Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC ke goyon baya. Haka Hon. Femi Gbajabiamila.
Sai dai kuma wannan bai haka Sanata Ali Ndume kalubalantar Lawan ba. Haka shi ma Hon. Umar Bago ya kalubalanci Gbajabiamila.
Daga a zaben 2015, APC ta ce a zabi Lawan da Gbajabiamila, amma Bukola Saraki da Yakubu Dogara suka nemi goyon bayan wakilan PDP, kuma suka yi nasara.
Daga baya su biyun duk suka koma PDP.
Discussion about this post