Mutane da yawa sun yi ta tofa albarkacin bakin su a bisa irin shigar da uwargidan shugaban kasa ta yi a wajen liyafar dare na murnar ranar dimokradiyya.
Shi dai wannan kaya mai dan karan tsada da Aisha ta saka an kiyasta kudinsa da zai kai akalla sama da dala 4000 da yayi daidai da Miliyan 1,544,440.
Ta fito a wannan rana tana taku yadi-yadi cikin kasaita tare da gwanin ta wato shugaba Buhari.
A dalilin tsadar wannan kaya mutane da dama da suka zanta da wakilin mu sun bayyana cewa irin wadannan kaya masu tsada bai dace ta saka su ba ganin cewa mutanen kasa da dama na fama da kuncin rayuwa.
Wasu kuma koma wa suka yi da rashin dacewa ta saka kaya irin haka ba tare da ta rufe jikinta ba.
Wannan dai mutane suka rika bayyana ra’ayin su.
Aisha dai ta burge a wannan taro kuma anyi taro an gama lafiya.
Discussion about this post