SHAYE-SHAYE: An kama mai sarrafa Kodin din karya a Bauchi

0

Rundunar ‘Yan sandan jihar Bauchi ta kama wani Emmanuel Patrick dake sarrafa maganin Kodin na karya a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Datti Abubakar ya bayyana cewa jami’an sa sun tarke Emmanuel ne a wani Otel yana dura wani ruwan magani wai Kodin a cikin kwalabe.

Datti ya ce wasu ne suka sanar ‘yan sanda a asirce kafinnan suka diran masa adaidai gogan naka na faman ciccika kwalaben da ruwan maganin.

Shi dai wannan ruwan magani da yake duddurawa ba a san kona menene ba yake kwarmatsawa sannan ya siyarwa mashaya maganin a matsayin Kodin.

Sai dai kuma ‘yan sandan basu yi dace ba domin kuwa abokin aikin Emmanuel ya arce kafin ‘yan sandan su cimma su a Otel din.

Abubuwan da aka samu tare da Peter sun hada da kwalaben jabun Kodin da aka riga aka dura guda 71, kwalaben maganin tari na Tutolin 30,tukunyar ruwan Kodin da suka hada, kwalabe sama da 100 wanda babu komai a ciki da kuma takardar tambarin kamfanin kodin din na karya.

Shi dai Emmanuel ya amsa laifin sa inda ya nemi sassauci yana mai cewa shima rudin sa aka yi.

Share.

game da Author