An gano kwayoyin cutar shan inna a magudanar ruwan bahaya a karamar hukumar Tarauni a jihar Kano.
Bayanai sun nuna cewa jihar Kano ta yi shekaru uku kenan rabon da aji wani ya kamu da cutar a jihar.
Ma’aikacin hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko dake karamar hukumar Tarauni Nura Haruna ya sanar da haka wa manema labarai.
Haruna yace duk da cewa wannan irin cutar shan inna da aka gano a magudanar ruwan bahaya bamai nakasa bangaren jikin mutum bane amma zai iya rikidewa ya zama haka idan ba a maida hankali wajen gaggawar kau dashi ba.
Ya ce hukumar su na zargin cewa shigo da cutar aka yi Zariya ko kuma rashin tsaftace muhalli ne ya bullo da cutar.
” A kwanakin baya mun samu rahotan cewa cutar ta bullo a Zariya da haka ya sa muke zaton cewa wasu yara dake dauke da cutar suka shigo da ita Kano.
Domin hana yaduwar cutar gwamnati za ta yi wa yaran dake karamar hukumar Tarauni gaba daya allurar rigakafi.
MUTANE SUN KI YARDA A YI WA ‘YA’YAN SU ALLURAN RIGAKAFI DIN
Haruna yace bayan an fara bin mutane gida gida domin yi wa yara allurar iyaye da dama sun hana a yi a ‘ya’yan su allurar.
Ya ce wadannan iyaye ba jahilai bane ballantana ace rashin sani da rashin ilimin boko ne ya sa suka hana ayi wa ‘ya’yan su allurar.
” Akwai likitoci, ma’aikatan kwastam, ‘yan sandan da suka hana a yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafin cutar. Duk da haka mun sami matan da suka bada ‘ya’yan su ba tare da izinin mazajen su ba a boye.
Haruna ya yi kira ga gwamnati da ta saka baki a cikin wannan matsalar da suke fama da shi domin rashin yi wa yaran allurar rigakafin na iya zama aikin banza.
KORAN MA’AIKATAN WUCIN GADI
Haruna yace hukumar ta kori wasu ma’aikatan wucin gadi da aka dauka domin yi wa yara allurar rigakafi.
Ya ce ma’aikatan da suka kora sun kai 12 a dalilin karyar yi wa yara allurar rigakafi da aka kama su suna yi.
” Mun san cewa iyaye da dama sun hana a yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafin inda hakan ya sa wadannan ma’aikata yi wa yara shaidar yin allurar rigakafi bayan ba su yi musu ba.