Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato sun bayyana sabbin matakan da suka dauka domin tabbatar da cewa an gudanar da shagulgulan Sallah Karama cikin kwanjiyar hankali da lumana.
Kakakain Yada Labarai na Rundanar, Terna Tyopev, ya ce za a yi amfani da jami’an tsaro 2,181 domin karfafa tsaro a lokacin bukukuwan sallah.
Wannan mataki kamar yadda ya bayyana, ya biyo bayan wani taron musamman da jami’an tsaro suka gudanar a ranar Juma’a, 31 Ga Mayu, tare da masu ruwa da tsaki, har ma da shugabannin bangarorin addinai.
Jami’an tsaro sun kuma haramta yin amfani da ba-toyi, wato ‘knockouts’ da sauran abubuwan da yara ke fasawa ya na kara a lokacin bukukuwa.
Sannan kuma ya ce an haramta zirga-zirgar Keke NAPEF a cikin Jos da Bukuru a lokacin. Kuma duk wanda ya karya wannan doka, to za a hukun ta shi.
Daga nan kuma ya ce masu zuwa Sallar Idi su ajiye motocin su kimanin mita 100 nesa da masallacin Idi.
A karshe sanarwar da jami’an tsaron ta fitar, ta nemi jama’a su bada hadin kai domin a samu damar yin shagulgulan Sallah cikin natsuwa, rashin cinkoso da kuma cikin kwanciyar hankali.