A yau Alhamis ne majalisar dokoki na jihar Kaduna ta zabi kakaki da mataimakin kakakin majalisar jihar.
Aminu Shagali da ke wakiltar karamar Sabon Gari wadda shine kakakin majalisar a wancan zangon aka sake zaba kakakin majalisar.
Yusuf Zailani wanda wannan shine karon na hudu yana dawowa majalisa ya zama mataimakin majalisar.
Zailani yana wakiltar karamar hukumar Igabi ne a majalisar.
Wannan shine karo na farko tun dawowar dimokradiyya a 1999 za ayi shugaba da mataimaki duk ‘yan yanki daya.
A wannan karon ma makwabta.
Da yawa daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakin su a kan wannan zabi na Shagali da Zailani sun ce ba a yi adalci wa wasu sassan jihar ba.